Shawarwarin yadda za a kara bunkasa harshen Hausa

A halin yanzu rubutun Hausa ta fannin adabin zube, wasan kwakwayo da sauransu ya samu nakasu matuka. Kusan ko su wadanda Hausar ita ce ainahin harshensu suna da matsaloli da suka shafi yadda za su tallafe ta har ta ci gaba da bunkasa a matsayin rayayyan harshe. Kodayake masu rubutu irin na soyayya suna bakin […]

Shawarwarin yadda za a kara bunkasa harshen Hausa

A halin yanzu rubutun Hausa ta fannin adabin zube, wasan kwakwayo da sauransu ya samu nakasu matuka. Kusan ko su wadanda Hausar ita ce ainahin harshensu suna da matsaloli da suka shafi yadda za su tallafe ta har ta ci gaba da bunkasa a matsayin rayayyan harshe.

Kodayake masu rubutu irin na soyayya suna bakin kokarinsu kuma masu turakun yanar gizo su ma suna yin nasu kokarin. To, amma duk wadannan suna bukatar kara kwazo sosai domin ci gaban harshen Hausa da masu magana da shi a ko’ina a duniya.

Wani abin mamaki da wannan harshen ya watsu sosai a duniya, kusan a duk nahiyoyinmu in dai akwai jami’a a kasa uku zuwa biyar, sai ka ga ana nazarin Hausa. Bugu da kari, mafi yawan kasashen wannan nahiya tamu ana amfani da Hausa kuma tana tasiri wajen kasuwanci da addini da ilmi.

Kusan ganin haka ne na ga ya zama dole a jajirce wajen maido nazarin ta da raya ta da gina ta a matsayin cikakken harshe mai rayuwa. Za mu cin ma wannan burin ne ta hanyar nazarin ta tun daga gida da kananan makarantunmu. Kuma a ci gaba da nazarin ta a manyan makarantunmu, sannan a rika sanya gasa ta rubutu; a sa kyauta domin jawo hankalin marubuta.

Za mu hada kanmu domin tanadar kyautar, za mu iya tuntubar hukumomi domin samun tallafi wajen bayar da kyauta. Ina ganin in dai yawa wani abu ne, in Hausa ta bunkasa za ta iya zama harshen kasa, wanda zai karbu ga kowa-da-kowa. To, amma samun haka ba zai yiwu ba sai masoya harshen da duk mai yin harshen ya sa hannu.

Wani abin sha’awa, Hausawa na aron kalmomi daga Larabci da Turanci da Yarabanci da sauransu, to amma wannan sam bai bata Hausa ba. Mu masu yin amfani da harshen, mu ne ya kamata mu sa garkuwa mu ba shi garkuwa ta tsare shi daga dukkan kalubale na canjin yanayi kamar sutura, abinci da sauransu. Mu yi komai a hausance in dai bai ci karo da addininmu ba.

Jaridun Hausa kamar su ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ da ‘Aminiya’ da ‘Leadership A Yau’ ya kamata mu rungume su ta hanyar sayen su, mu kuma karanta sannan mu rika aikawa da gudunmuwarmu don kara ingancinsu.

Yaranmu, mu rika koya musu karatun Hausa da fadakar da su muhimmancin harshen, domin koyon addini, kasuwanci da al’adu da sana’o’i. Kuma mu gwada masu lallai naka shi ne naka. Mu rika saya masu littattafan Hausa irin su ‘Ruwan Bagaja’ da ‘Magana Jari Ce’ da ‘Jatau Na kyallu’ da ‘Bala Da Babiya’ da sauran littattafai masu ma’ana.

A nan, ina amfani da wannan dama domin gode wa malamanmu na Jami’ar Bayero da sauran dukkan malamai na sauran jami’o’in gida da sauran kwalejojin ilmi wajen wannan kokarin. Haka kuma ina jinjina wa marubuta a jaridu da sauran kafafen sadarwa. Ina fatan Allah Ya sa mu dace, amin.

 

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta