Shawo kan hakar albarkatun kasa ba bisa ka’ida a Arewa ba
Kowace rana daruruwan jakuna da tifofi da kurar baro-baro na daukar kwanuka da shebur ana amfani da su wajen hakar miliyoyin ton-ton na kasa, inda ake kwashe su zuwa wuraren da akee aikin gina gidaje da sauran gine-gine a daukacin fadin kasar nan. Mutane da daman a nuna ko-in-kula kan hakar kasa mai tattare da […]
Kowace rana daruruwan jakuna da tifofi da kurar baro-baro na daukar kwanuka da shebur ana amfani da su wajen hakar miliyoyin ton-ton na kasa, inda ake kwashe su zuwa wuraren da akee aikin gina gidaje da sauran gine-gine a daukacin fadin kasar nan.
Mutane da daman a nuna ko-in-kula kan hakar kasa mai tattare da hadari: da ke zaizaye gonaki, ya kassara aikin gona da ake dadon wadata kasa da abinci, ta yadda manoma ke samun kudin shiga da dimbin hraji ga kasa. Noma ya matukar rage fatara da talauci da yakar yunwa. Baya ga cewa kamata ya yi a killacbe albarkatun kasa, ta yadda za a yi amfani da su yadda ya dace, kamata ya yi mazauna karkara sun illar da ke tattare da hakar kasa ba bisa ka’ida ba.
Nazari ya nuna cewa zaizayar muhalli na aukuwa ne sanadiyar hakar kasa da ake yi a wadannan al’umomi ba bisa ka’ida ba, tattare da kin tabbatar da dokokin kare muhalli.
Kusan a iya cewa boyayyen al’amari cewa mata na kwasar kasa su sayar a farashi mai rahusa, duk da hka akwai dimbin wurare da ake aikin gine-gine a wasu wurare, musamman a Abuja babban birnin Najeriya. Miliyoyin mutane har yanzu ba su fahimci illar da wadannan masu hakar kasa ke haifarwa na sauyin yanayi da kaurar da ake yi a kasarmu.
Sannan bincike ya nuna cewa rashin hana mutane hakar kkasa ba bias ka’ida ban a matukar taka rawa wajen lalata muhalli, ya haifar da dimbin matsalolin gurbata muhalli da ke cutar da rayuwa kimanin ’yan Najeriya miliyan 80.
Hakakr kasa ya tsananta ta yadda gonaki da dama a wasu sassan Arewa tuni aka yi watsi da su. bacewar gonaki shi ke haifar da wawakeken rami a wasu sassan. Illolin da lke gurbata muhalli suna da matukar tasiri kan yanayi da kassara tattalin arziki, ta yadda wuraren da kasar ta zaizaye ke haifar da asarar hatsi da tsirran da aka shuka.
Kodayake wasu jihohin sun kaddamar da hukumomin shawo kan hakar kasa ba bisa ka’ida ba, sannnan sun fara kai farmaki ga masu hada-hadar kasuwancin hakar kasa, inda ake kame masu wannan aiki ba bisa ka’ida ba, amma daukar mataki bai kankama ba, musamman a wuraren da ake fama da rashin aikin yi, inda kasa ta zama habnyar samun kudi a tsakanin matasan da ke keta doka.
Jihohi da dma sun bayar da lasisi ga kamfanoni su ci gaba da aikinsu bias tanadin doka, ba tare da daukar matakin da zai shawo kan illar sauyin yanayi da kaurar mutane.
Na fake a matsayin mai sayen kasa da yawa a wasu sassa na Abuja da Jihohin Kaduna da Filato, inda na gano yadda ake saka ’yan mata cikin harkar kasuwancin, wadanda ake dauko ssu daga makaranta, tun suna ’yan shekara 15 a taho da su wurin da ake hakar kasa don su rika kawo tan-tan ga kamfanonin aikin ggine-gine, wato aiki mai wahalar yi a rayuwa na satar kasa da ba zai dore ba, da ke tattare da dimbin illoli.
Da sassafe ranar Asabar na kira waniu abokin karatuna ya shirya mini yadda zan hadu da mutane da ke kasuwancin kasa a daya daga cikin kananan hukumomi yankin Arewa, inda al’ummomi da da dama ke fama da zaizayar kasa saboda wannan mummunan kasuwanci na hakar kasa. Da zuwanmu wajen sai shugaban mutanen, wanda ya san abokina ya yi masa korafin cewa mafi yawan yaransa suna zukar tabar wiwiwi, su tare a kan tarin kasar da suka hako lokacin da suke jiran abokin ciniki, wanda zai sayi tudun kasarsu. Mai l;aushi ko Mai tsakuwa.
Jibrin Dankasa wanda ya shahar a hada-hadar kasuwancin kasa ya koka da cewa “baya ga jakuna muna kai wa abokan huldarmu kasa da baro, har ma manyan motocin daukar kaya cikee ko rabi, kuma muna da ’yan ka yin a yi da ke shiga tsakani wajen samu abokan ciniki da ke sayar da kayanmu ga mutane daban-daban, har ma da wuraren da ake ytin gine-gine da yin tubali (bulon gini).” Da aka tambaye shi ko suna yin wannan kasuwanci ba tare da trakun saka da gwamnati ba, sai ya bayyana cewa, ‘al’amari na biyan mutane kudi a kowace rana.’
A cewarsa, kasuwanci na samar da kudi a kowace rana, “don haka biyan kudi kadan ga jami’an hukuma ba wata matsala ba ce. Kasuwancinmu na smaun tallafin kamfanonin gine-gginee, masu hada-hadar kasa da masu neman aikin yi a kasar nan. Muna samar da aikin yi ga ‘’yan Najeriya da ba su da aikin yi, musamman matasa,” inji shi.
dankasa ya yi ikrarin cewa iyaye da dama suna tturo ‘’ya’yuansu wajen aikin hakar kasa da sayar da ita a al’ummomi da dama, wadanda suka hada da ciki da wajen Jihar Kano.
Ya ce, “babu abin da ya sauya tun sa’adda na fara harkar kasuwancin da Naira 100 kacal a shekarar 1978. Kowace rana kimanin mutane 300 ke barin gidajensu da safe don zuwwa wajen hakar kasa a cikin ruwa ko tudu, inda suke amfani da kayan aiki na gargajiya, kodayake kadan ne daga mazan ke tifa, sauran na amfani da jakuna ne don samun saukkin dauka ba tare da hukuma ta hantare su ba. Saura kuwa sun dogara ne da zuwan jakuna su cika buhunhuna sumuntti da kasa sannan su dora wa baro don kai wa abokan kasuwancinmu daban-daban.
Muna sayar da cikin tifa kan Naira dubu 27; rabin tifa kan dubu Naira 13,500, kuma a wasu sassan muna sayarwa kan Naira25,000 da Na12,500. Buhun sumuntti na kasa da muke bai w abokin hulda a kan Naira 120, yayin da yaranmu da kee tura baro ke karbar naira 30 ko Naira 25 kan kowane buhu. Muna samun kudi kullum. Kana jin cewa idan aiki nike yi da gwmanati zan samu Naira 150,00 a kowace rana, in biya ma’aiakta 150 kowace rana ko mako abin da Za su kula da iyalansu.
Bayan dan tattaki daga wurin, sai na tunkari wani mutum wanda ke cikin ruwa yana debo kasa da shebur, ya yi fushi da ya gani dauke da kyamara/ sai ya fito daga ruwan ya bukaci in ba shi kyamarar, yana tambayar dalilin da ya sa nike daukar hoto.
Na dai samu sa’ar shawo kansa ceewa babu hotonsa a ciki kyamarar. Sai uya bukaci sanin dalilin zuwana wurin dfa kyamara, ba tare da izininsa ba. Abokina wwadanda masoyin kungiyar kwallon Arsenal ne, sai ya lallaba shi ya ba shi hakuri, inda ya bayyana masa cewa a matsayinsa na dalibi mai nazarin albarkatun kasa da taswirarta yana neman nau’ukan kasa ne don aikin da aka ba shi a makaranta, kuma wannan ne dalilinmu na zuwa nan.
Ya fada masa cewa za a samu karuwa daga shawararsa. Saya ya bude kwalin taba ya ba shi kara guda, sai suka fara sha suna jin dadi. Sai na yi amfani da wannan damar na tattauna da shi kan matsalar yanayi, da yadda za a hadu da mutane daban-daban a tunkari matsalar.
Sai Na ce: |na ji cewa kuan hana ’ya’yanku zuwa makarantta; a wasu lokutan ma kukan kawo nan su yi hada-hadar hakar kasa. Wannan aikin na cutar da lafiyarku, musamman shiga cikin rruwa ba tare da rrufafffun takalma ba. Kuna illata lafiyarku, ta yaddda hadarin da kee tattare da aikinku na iya kassara tsawon rayuwwarku.
“Idan kuka bayar da hadin kai wajen shawo kan sauyin yanayi, ku kauce wa hadurrran da kuke fuskanta a kullum, ku yi kokkarin zama a rukunin masu kokarin kawo sauyi, matukar kuna so rayuwarku ta inganta ku yi nisan kwana, ku kuma tura ‘’ya’yanku makaranta kullum don samu ilimi mai amfani a kyakkyawan muhalli.” Daga nan sai na fito da wani dan littafin rubutu: na koyon Ingilishi da Larabci da karamar jakkatar makaranta na ce kana iya bai wa ‘’ya’yanka.
Samar da abinci ta hanyar aikin gona
Na gana da wasu manoma wadanda gonakinsu zaizayewar kkasa ta far musu sanadiyyar aikin hakar kasa da gine-gine mabambanta, al’amarin da ya haifar da takkaddama tssawon shekaru. Sun koka cewa a Najeriya ne kawai wadannan al’amura kee faruwa.
Ardo Sani, wani makiyayi cewa ya yi, ba ni da ilimin zamani ammma ina sauraren rrediyo tsawon shekara 25, don haka nasan cewa kasashen da suka ci gaba suna yaki da miyagun da ke hakar kasa a kusa da gonaki ba tare da izinin hukumomi ba. A wasu kasashen da suka ci gaba kasa na da matukar darajar kadara mai kima.
Ma fada masa manufata ita ce rubuta labaran da za su taimaka wajen shawo kan matsalar wssauyin yanayi a al’ummominmu ta hanyar yadawa a kafafen yada labarai. Muna bukatar ilimantar da su domin miliyoyin manoman Najeriya na bukatar tashi tsaye haikan wajen shawo kan dumamar yanayi.
Mafi yawan kwararrun masana kan muhalli da na tuntube su ssun ce “shawo kan wannan babban kalubale da ya addabi al’umma, na bukatar a hada da tsarin wadata kasa da abinci kan yadda illarsa za ta cutar da dimbin mutane, har ta kai ga sun fara yin kaura daga wannan wuri zuwa wancan; rikicin kan iyakar kasa tsakanin makiyaya da manoma, ind amasu hakar kasa da manoma ke takun saka daga wannan wuri zuwa wancan sai yin kaura don neman kwadago da illarsa.
kwararru da dama na da ra’ayi iri guda don haka suka yi kira ga hukumomin gwamnati da su tsara wwani sshiri da za aaiwatar da bayar da horo ga masu horarwa kan illar da ke tattare da suyin yanayi, inda za a samu daidaito a tsakanin al’umma; don nuna mussu abin da ya dace. Su fitar da managarciyar taswirar tsarin da ya dace da halin da ake ciki don warware matsalolin da ke addabar gonaki da yadda za a shawo kan sauyin yanayi, sannan a kara kyautata zamantakewar al’ummomi; a samar da kafar ilimantarwa kan sauyin yanayi a tsakanin yara masu tasowa. Sannan a inganta dabarun wadata al’umma da abinci da tallafa wa ma’aikata da za su yi aiki wajeen shawo kan sauyin yanayi da dabarun noma a Najeriya, sannan a kara fadakarwa kan muhimmancin ilimin ‘’ya’ya mata da tallafa musu wajeen shawo kan sauyin yanayida fadada fahimtar al’umma kan yadda za a bunkasa zamantakewa.
Masana da kwararru kan inganta gandun daji sun dade suna kira ga hukumomin gwamnati da su kara kokari wwajen dasa miliyoyin tsirrran bishiyoyi don samar korayen tsirrai sun baibaye kasa, don samar da gonaki da samun kyakkyawan sauyin yanayi a nan gaba.
Sun jajirce kan lallai gwamnati da kafafen yada labarai sun bullo da shirye-shirye musamman wadanda ke da tasirin fadakar da al’umma hadurrran d ake tattare da sauyin yanayi da bukatar da ake da ita ta hadin gwiwar daukacin al’umma wajen shawo kan matsalar.