Shaye-shaye Ke Rura Matsalar Tsaro A Yobe —Sarkin Fika

Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun kwayoyi a matsayin abin da ke rura wutar rashin tsaro a jihar. Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin wata liyafa da ya shirya ga ’yan jarida a fadarsa da ke Karamar Hukumar Potiskum. Ya ce […]

Shaye-shaye Ke Rura Matsalar Tsaro A Yobe —Sarkin Fika

Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu IIdriss

Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun kwayoyi a matsayin abin da ke rura wutar rashin tsaro a jihar.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin wata liyafa da ya shirya ga ’yan jarida a fadarsa da ke Karamar Hukumar Potiskum.

Ya ce harin baya-bayan nan da aka kai a yankin Gurjaje da ke Karamar Hukumar Fika ta jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya tare da lalata gidaje sama da 100, ya tabbatar masa da alakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da rashin tsaro.

Sarkin Fika ya bukaci gwamnatin jihar da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta fito da tsare-tsaren da za su dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da cigaba a yankunan da lamarin ya shafa, yana mai kokawa kan tabarbarewar tattalin arziki a kasar.

Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro

Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya 

Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn

Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce Habasha