Shaye-shaye tubalin ginin kazamar al’umma

A duk lokacin da aka ambaci kalmar shaye-shaye ba ta bukatar wani dogon bayani domin mafi yawan mutane za su fahimci abin da ake nufi. Shaye-shaye abu ne sananne ga al’umma cewa, ‘matasa maza su suka fi yawa a cikin harkar,’ wani sa’ilin a kan samu ‘yanmata duk da cewa su ‘yanmata sun fi ta’ammali […]

Shaye-shaye tubalin ginin kazamar al’umma

A duk lokacin da aka ambaci kalmar shaye-shaye ba ta bukatar wani dogon bayani domin mafi yawan mutane za su fahimci abin da ake nufi. Shaye-shaye abu ne sananne ga al’umma cewa, ‘matasa maza su suka fi yawa a cikin harkar,’ wani sa’ilin a kan samu ‘yanmata duk da cewa su ‘yanmata sun fi ta’ammali da kayan maye na kwayoyi ko magunguna na ruwa. Wasu mutanen idan suka gawurta abin ya yi nisa sukan yi amfani da allura, ta hanyar yi wa kansu duk don su yi maye.

Kullum za ka ji ana fadin ana yaki da wannan dabi’a mummuna, wadda haka ne ma ya sa aka samar da Hhukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi (NDLEA), amma har yau abin kamar kara zuga matasa ake, maimakon su daina sai dai a rika samun sabbbi suna shiga harkar. Hukumar NDLEA ta kan kama matasa, tare da azabtar da su wani sa’ilin azabtarwar ta kan zama silar mutuwar wasu. 

A garin da nake wato Hadejia wannan hukuma ta zama silar mutuwar wasu a baya, sakamakon takan kai samame wani waje da ake kira da suna HAUSAWA a bakin kogi, wanda ya kasance waje ne da matasa ke baje kolinsu na shaye-shaye. Idan jami’an hukumar suka kai samame wajen su kuma matasan kan neman hanyar tserewa, wanda hakan ke sa wasu fadawa kogi da niyar guduwa, to mutumin da ke hali na maye ina shi ina iyo a kogi? Wani kuma dama can bai iya ba, idan kwana ya kare shi ke nan rai sai ya yi halinsa, Allah Ya saukaka. 

Sakaci daga wajen iyaye na rashin kula da tarbiyyar ‘ya’yansu ita ce babbar matsalar da ke jefa matasa harkar shaye-shaye, sakamakon rashin sa’ido akan irin abokan da suke mu’amala da su. Sai uwa uba ‘yan siyasa, wadanda sukan saya wa matasa kayan mayen domin su ji dadin sa matasan ayyukan assha, saboda sun sani duk wanda yake cikin maye zai iya aikata kowane irin aiki komai muninsa, ba tare da la’akari da abin da zai biyo baya ba. Hausawa dai sun ce, ‘gani ga wane ya ishi wane tsoran Allah.’ 

Matasa ya kamata mu ajiye wannan mummunar dabi’a dalilina shi ne zai yi wahala ace ba ka san wani wanda ya haukace ta dalilin shaye-shaye ba, ko za ka so a ce yau an wayi gari kana yawo a bola ta dalilin maye da ka dora wa kanka sakamakon ka haukace? Idan ka mutu ka tarar da Mahaliccinka, wace amsa ka tanada ta kare kanka, idan ya ce me ya sa kake maye a duniya har ya zama silar haukacewarka? 

Matukar ana son kawar da wannan dabi’a ta shan miyagun kwayoyi dole a taka wa ‘yan siyasa burki da ke bata rayuwar matasa, ta hanyar haramta musu neman mulki, su kuma iyaye su bai wa ‘ya’yansu tarbiyya yadda ya kamata su rika kula da irin abokan da suke mu’amala da su. 

Gwamnati ita kuma sai ta yi kokari wajen inganta rayuwar talakawanta da ababen more rayuwa, matasa kada a bar su a zaune gari banza saboda barin tarin matasa a zaune gari banza zai iya haifar da kowane irin nau’in matsaloli ba sai na shaye-shaye kadai ba. Ku kuma hukumar NDLEA duk garin da kuke kun san manyan dilolin garin, kun san na Jiha, don haka sune mutane da ya kamata ku fara takawa burki, ta hanyar hana su fataucin miyagun kwayoyin, sannan sai ku taka wa matasa burki. Shaye-shaye ne tubalin ginin kazamar al’umma, Ya Allah Ka kare mu, Ka sa mu gama da duniya.

Kainuwa ya rubuto makalarsa daga Hadejia Jihar Jigawa. Za a iya tuntubar marubucin ta: 08100229688/09073801967 Nasiru Kainuwa Hadejia <[email protected]