Shaye-shayen miyagun kwayoyi ga matasa: Ina mafita (3)

  ALHAJI IBRAHIM AHMAD KATSINA shi ne Shugaban Gidauniyar Samar da Zaman Lafiya ta Fannin Tsaro da Zamantakewar Al’umma. Shi ne Babban Bako Mai jawabi a yayin taron Kungiyar Gizago ta Kasa da aka gudanar a Katsina a ranar Asabar22-09-2018, inda ya gabatar da wannan takarda dangane da illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi; ga kashi  […]

Shaye-shayen miyagun kwayoyi ga matasa: Ina mafita (3)

 

ALHAJI IBRAHIM AHMAD KATSINA shi ne Shugaban Gidauniyar Samar da Zaman Lafiya ta Fannin Tsaro da Zamantakewar Al’umma. Shi ne Babban Bako Mai jawabi a yayin taron Kungiyar Gizago ta Kasa da aka gudanar a Katsina a ranar Asabar22-09-2018, inda ya gabatar da wannan takarda dangane da illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi; ga kashi  na karshe:

Illolin miyagun kwayoyi ga rayuwar matasa: Tu’ammali da miyagun kwayoyi babbar annoba ce da ke lalata mutunci da diyaucin matasa, kamar yadda take illata kwakwalwa da lafiyarsu. Kamar yadda masani Perkinson (2002) ya bayyana, giya ko kayan maye na illata tsarin gudanar jini a kwakwalwa da sassan jiki, wanda haka kan haifar da dakikanci ko rashin fahimtar karatu. Don haka matasan da suka zama ’yan kwaya, sukan rasa karsashin fuskantar neman ilimi ko koyon wata sana’a ko aiki. Haka kuma tu’ammali da miyagun kwayoyi da kayan maye kan illata kwakwalwa ko rage mata karfin aiki a jiki, kamar yadda hakan kan rage kaifin tunani, wanda kan shafi batun neman ilimi a makaranta. Mafi yawa daga irin wadannan kwayoyi kan haddasa wa matasa koma-baya, su zama cima-zaune, wadanda ba su iya tsinana wa kansu komai. Wannan kuma kan sanya mugun tunani ga matasan, su rika jin sha’awar aikata mugun aiki, kamar sata, fashi da makami da sauransu. Tu’ammali da kwayoyi kan sanya matasa su rika jin wani nishadi da karsashi na dan lokaci, daga bisani kuma su zama masu karkataccen tunani, su zama hadari masu ban tsoro ga al’ummarsu.

Wasu daga cikin illolin miyagun kwayoyi a takaice sun hada da:

1-Shafar lafiyar kwakwalwa da karkatar da tunani zuwa mara kyau.

2-Haddasa aikata manya da kananan laifuffuka a cikin al’umma, kamar rashin gaskiya, cin amana, sata, fashi da makami, garkuwa da mutane don amsar kudin fansa, ta’addanci da sauransu.

3-Kassara hanyoyin jini da zuciya, wanda haka kan haifar da munanan cututtuka ga jiki.

4-Sanya mugun kudiri, mugun tunani a zuciya, wanda haka kan haifar da hauhawa da tafasar zuciya.

5-Kawo tarnaki ga ci gaban matashi, domin kuwa duk matashin da ya zama dan kwaya, lalacewa yake ya zamanto marar amfani ga kansa da al’ummarsa.

6-Haddasa cututtuka daban-daban ga mai tu’amali da ita, wanda hakan kan rage masa tsawon rayuwa. Koda mutum ya rayu, rayuwar za ta zama marar amfani, domin rayuwa ce ta rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Bincike dai ya karkare da cewa babu wata annoba da ke haifar da illa ga al’umma kamar tu’amali da miyagun kwayoyi. Duk wani mugun laifi, tushensa na like da miyagun kwayoyi da kayan maye. A lokacin da mai niyyar aikata laifi ya kudiri niyyar aikata laifi, da zarar ya sha kwaya yakan samu karkataccen tunanin da zai ingiza shi ga cimma bakin burinsa.

Babu shakka lokaci ya yi da shugabannin al’umma za su tashi tsaye domin dakile annobar tu’ammali da miyagun kwayoyi da kayan maye a cikin al’umma. Wannan ya zama wajibi musamman idan aka yi la’akari da yadda wani sakamakon bincike ya nuna, inda a wasu wuraren ake samun matashi daya daga cikin matasa goma da ke tu’ammali da kwaya, ake samun uku cikin goma da ke shan sigari, ake samun daya cikin ashirin da ke shan wiwi. Haka kuma an samu wani rahoto da ke nuna cewa, kashi 20 cikin 100 na na tu’ammali da sauran kayan maye, musamman kodin tiramadol, shisha da sauran dangoginsu.

Kalubalen al’umma: Akwai babban kalubale ga al’umma dangane da tu’ammali da miyagun kwayoyi da sauran kayan maye. A lokacin da aka samu matasa a cikin al’umma suna tu’ammali da kwaya, lallai ne a san hanyoyin da za a bi wajen rage laifin al’amarin, kada a bijiro da wasu muyagun dabi’u da za su ta’azzara batun.

A daina kyara ko kyamar matasan da suka tsunduma cikin tu’ammali da kwaya. Maimakon haka, ya kamata a kusance su, a jawo su jika, a rika ba su magana da lallashi. Sannan a rika yi musu jagora da nasihohin karfafa gwiwa, domin su gane aibin kwayar domin guje mata. Idan kuwa aka ce za a rika zaginsu ko la’antarsu, za su kara kekashewa ne, su tunzura, su bijire wa al’umma.

Akwai kalubale ga iyaye, cewa lallai ne su tashi tsaye su sauke nauyin da Allah Ya dora musu na kula da tarbiyyar yaransu. Lallai ne iyaye su kula da yanayin halayen ’ya’yansu, su dauki matakin gyara tunda wuri idan sun lura da canji. Haka kuma, iyaye ya kamata su kula da irin abokan da ’ya’yansu ke mu’amala da su. Da zarar ba su amince da tarbiyyar abokan ’ya’yansu ba, sai su yi saurin daukar matakin raba su, tare da ankarar da iyayen wadancan yaran, domin su ma su kula. Iyaye su guji nuna shagwaba ga ’ya’yansu fiye da kima. Kuma su daina barin tarbiyyar yaransu ga ’yar raino, su rika tattaunawa da ’ya’yansu, suna jawo su a jika domin sanin halin da suke ciki. Su kula da su a gida, kuma su rika bibiyar al’amuransu a lokacin da suke makaranta. Su yi kokarin ba su jagora na kirki, su tantance musu abubuwa masu kyau da marasa kyau.

Lallai ne shugabannin al’umma, musamman ’yan siyasa su canja alkiblarsu, domin kuwa akwai zargi mai yawa a kansu, yadda suke daure wa matasa gindi, wajen ingiza su ga shaye-shaye, suna sanya su ayyukan daba domin yakar abokan adawarsu.

Domin tsabtace al’umma da raba ta da tu’ammali da miyagun kwayoyi, babu shakka ya kamata a hada hannu a yaki al’amarin kai-tsaye ba tare da bata lokaci ba. Ya dace a hada kai da hukumomin lafiya da jami’an tsaro da shugabannin al’umma na zamani da na gargajiya da malaman makaranta da malaman addini, domin shata hanyoyin da suka kamata wajen yaki da wannan annoba ta shaye-shaye.

Ya kamata a samar da dokokin da suka dace na hanawa da hukunta masu kunnen kashi da suke shigowa da sayar da haramtattun  magunguna a cikin kasa. Kuma a samar da kwamitocin bibiyar al’amuran matasa, domin magance wannan annoba, musamman a samar da ayyukan yi da sana’o’i ga matasa da hanyoyin nishadi da shakatawa da suka dace, domin shagaltar da su daga zaman kashe wando, wanda ke jefa su ga shaye-shaye.

Su kansu matasa, ya dace su gane cewa rayuwarsu ta yanzu ita ce nasara ko akasin nasara ga rayuwarsu ta gobe. Don haka ya dace su yi koyi da shugabanni na kwarai da suka samu nasarar rayuwa, matukar suna son kasancewa shugabanni nagari a rayuwarsu ta gaba. Tu’ammali da kwaya dai babbar annoba ce, ya kamata a guje ta kuma a yi duk mai yiwuwa domin taka mata burki domin saita tsarin al’umma.

 

Mun kamala