Shegiya karya!
Wata yarinya ce ’yar karya, ta zo wani shago domin sayen ruwan Faro. Ta ce a ba ta ruwan Faro, aka ce mata babu. Sai ta ce: “Wash Allah, yau da me zan dafa wa saurayina abinci?” Akwai wani saurayi yana zaune a gefe, ashe ya ji ta. Sai ya mike shi ma ya zo […]
Wata yarinya ce ’yar karya, ta zo wani shago domin sayen ruwan Faro. Ta ce a ba ta ruwan Faro, aka ce mata babu. Sai ta ce: “Wash Allah, yau da me zan dafa wa saurayina abinci?” Akwai wani saurayi yana zaune a gefe, ashe ya ji ta. Sai ya mike shi ma ya zo ya ce a ba shi rowan Faro; aka ce masa babu. Sai ya ce: “Wash Allah, yau da me zan yi wanki?” Yarinyar ta yi murmushi ta ce wa saurayin: “Ka ga ni ma Faro na zo saye wai babu.” Shi kuwa ya ce to su je gaba ko za su samu. Suka canja wani shagon, nan ma aka ce musu babu. Suka yanke hukuncin cewa su hakura kawai. Har za su tafi sai saurayin ya ce ta ba shi lambarta, don su rika gaisawa. Sai yarinyar nan ta dauko takardar Naira dubu daya da biro ta rubuta lambar a jiki, ta ba shi. Shi kuwa da ya karba sai ya yage iya lambar da ta rubuta, ya mika mata ragowar takardar Naira dubun, ya ce: “Amshi, na yage iya lambar, saboda wannan takardar za ta yi mani nauyi a aljihu.”
Daga Abdullahi Lawal danbaba kayauki