Shehin Limaman Haramin Makka da Madina ya rasu
A ranar Litinin da ta gabata ce birnin Madina da ke Saudiyya ya shiga alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Al-Makari Khalili Abdurrahman Al-kari, Shehin limamai da dama da suke jan Sallah a Haramin Makka da Madina. Marigayin wanda aka haife shi a garin Muzaffarabad da ke kasar Pakistan a 1940 ya yi […]

A ranar Litinin da ta gabata ce birnin Madina da ke Saudiyya ya shiga alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Al-Makari Khalili Abdurrahman Al-kari, Shehin limamai da dama da suke jan Sallah a Haramin Makka da Madina.
Marigayin wanda aka haife shi a garin Muzaffarabad da ke kasar Pakistan a 1940 ya yi karatu a hannun Sheikh Muhammad Sulaiman a Lahore da Sheikh kari Anwarul Hak, inda ya haddace Alkur’ani Mai girma a wurin Sheikh kari Fadal Karim, sannan ya karanta ruwayoyin Alkur’ani daban-daban a wurin malaman Pakistan har ya shiga daya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi da ke birnin kafin ya fara aiki a matsayin mai karanta Alkur’ani a gidan rediyon Muzaffarabad.
A 1963 ne ya yi hijira zuwa Makka Mai girma, kuma ya karantar a Masallacin Bin Laden da kuma Masallacin Harami a bayan Sallar Asuba. Ya rika karantar da dalibai masu son haddace Alkur’ani.
Daga baya ya koma Madina inda aka nada shi malami a cibiyar ilimi ta Madina da ke karkashin kular Jami’ar Musulunci ta Imam Muhammad bn Sa’ud, a nan ya ci gaba da zama yana karantar da Alkur’ani Mai girma.
Daga cikin dalibansa akwai marigayi Sheikh Muhammad Ayyub Limamin Masallacin Annabi (SAW) da ’ya’yansa Sheikh Muhammad Khalil Al-kari Limamin Masallacin Annabi (SAW) da Sheikh Mahmud Khalil Al-kari, Limamin Masallacin kiblataini. Sauran almajiransa sun hada da marigayi Sheikh Aliyu Jabir, Limamin Haramin Ka’aba da Sheikh Aliyu bn Abdurrahman Huzaifi Limamin Masallacin Annabi (SAW) da Sheikh Abdullahi Basfar, Shugaban Hukumar Haddar Alkur’ani ta Duniya da Sheikh Usman As-Siddiki, Shugaban Kwamitin Kula da kungiyoyin Haddar Alkur’ani na Saudiyya kuma daya daga cikin wadanda suka kakkafa makarantun haddar Alkur’ani a Daular Saudiyya.