Shehu Malami ya rasu yana da shekara 85
Alhaji Shehu Malami — tsohon Sarkin Sudan na Wurno, babbar sarauta a Fadar Sarkin Musulmi — ya rasu a kasar Masar yana da shekara 85
Allah Ya yi wa tsohon Jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, Alhaji Shehu Malami, rasuwa yana da shekara 85.
Alhaji Shehu Malami — tsohon Sarkin Sudan na Wurno, babbar sarauta a Fadar Sarkin Musulmi — ya rasu ne a birnin Alkahira na kasar Masar, bayan gajeruwar rashin lafiya.
- Mutum 9,227 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Najeriya — FRSC
- An kashe kasurgumin dan bindiga Madaki Mansur da wasu 11 a Bauchi
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kdsuwa da rasuwar, ta wata sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar.
Sanarwar da hadiminsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin ta ce, Buhari, “Na kadu matuka da wannan babban rashi, wanda babban tuni ne cewa rayuwa ba ta da tabbas.
“Marigayin jagoran kasuwanci ne a duniya, wanda kuma ya yi amanna da karfin tattalin arzikin Najeriya.
“Babban saraki ne kuma jigo a bangaren masana’antu da raya al’adun gargajiya.
“Rasuwarsa babbar asarar ce ga Najeriya kuma muna mika ta’aziyya ga iyalansa da Fadar Sarkin Musulmi da al’ummar Jihar Sakkwato.
“Allah Ya jikan sa da arahamma.”