Shehu Sani ya koma PRP
Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya sanar da cewa ya koma Jam’iyyar PRP. A kwanakin bayan ne sanatan ya sanar da cewa ya fice daga APC, bayan jam’iyyar ta amshe takara daga hannunsa inda ta ba Uba Sani. Tun lokacin ya sanar da cewa zai sanar da jam’iyyar da […]
Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya sanar da cewa ya koma Jam’iyyar PRP.
A kwanakin bayan ne sanatan ya sanar da cewa ya fice daga APC, bayan jam’iyyar ta amshe takara daga hannunsa inda ta ba Uba Sani. Tun lokacin ya sanar da cewa zai sanar da jam’iyyar da ya koma, sannan ya kuma ya tabbatar da cewa lallai zai yi takarar sanata.