Shehun Bama ya kwanta dama
Daya daga cikin manyan sarakunan jihar Borno, Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibni Umar Elkanemi ya kwanta dama. Marigayin mai shekara 63, ya rasu ne da yammacin ranar Litinin 27 ga watan Afrilu 2020 a wani asibiti a Maiduguri babban birnin jihar Borno. Marigayin shi ne Shehun tsohuwar masarautar Dikwa na bakwai, wacce ta hadar da […]
Daya daga cikin manyan sarakunan jihar Borno, Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibni Umar Elkanemi ya kwanta dama.
Marigayin mai shekara 63, ya rasu ne da yammacin ranar Litinin 27 ga watan Afrilu 2020 a wani asibiti a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Marigayin shi ne Shehun tsohuwar masarautar Dikwa na bakwai, wacce ta hadar da kananan hukumomin Dikwa, da Ngala sai Kala-Balge.
A shekarar 2010 ne aka raba masarautar gida biyu wato masarautar Bama da Dikwa wadanda manyan sarakuna biyu ke mulka zuwa yanzu.
A cewar kwamishinam al’amuran cikin gida da al’adu tare da yada labarai na jihar Borno Babakura Abba Jato, marigayin ya rasu ne bayan ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya kamar yadda masu yawan shekaru irin nasa kan yi fama.
Babakura Abba, ya ce, fadar masarautar Bama zata sanar da lokacin da za a yi jana’izar marigayin.