Shehun Dikwa ya riga mu gidan gaskiya
Wannan ne dai karo na uku da manyan sarakunan jihar suke mutuwa a lokacin da babu tazara a tsakani
Shehun Dikwa, Alhaji Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi
Shehun Dikwa a jihar Borno, Alhaji Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi ya riga mu gidan gaskiya.
Sakataren Gwamnatin jihar Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya sanar da rasuwar a gari Biu, jim kadan da bayar da sandar mulki ga sabon sarkin na Biu, Alhaji Mustapha Umar Mustapha wanda Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya jagoranta ranar Asabar.
Ya rasu ranar Juma’a, kwana daya bayan an garzaya da shi wani asibiti a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wannan ne dai karo na uku da manyan sarakunan jihar suke mutuwa a lokacin da babu tazara a tsakani, ciki har da Shehun Bama da Sarkin Biu wadanda suka rasu a shekarar 2020.
Wani daga cikin manyan masu rike da sarauta a fadar ya tabbatarwa da wakilinmu a Maiduguri cewa za a gudanar da sallar Jana’izar basaraken ne a fadar Shehun Borno dake Maiduguri da misalin karfe 5:00 na yammacin Asabar.