Shehun malamin likitanci Farfesa Umaru Shehu ya rasu
Malamin malaman aikin likitanci kuma shugaban farko na Sashen ‘Community Medicine’ a Jami’ar ABU, Farfesa Emiritus Umaru Shehu ya rasu yana da shekara 97
Allah Ya yi wa babban shehun malami a fannin aikin likita Farfesa Umar Shehu rasuwa yana da shekaru 97 bayan gajeruwar rashin lafiya.
Marigayi Farfesa Emiritu Umaru Shehu shi ne Shugaban Sashen Aikin Likitan Al’umma na farko a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma tsohon ma’aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Ya koyar a jami’o’i daban daban a kasashen duniya kuma tsohon kantoman Jami’ar Maiduguri ne; tsohon Shugaban Jami’ar Najeriya ta Nsukka, sannan tsohon Uban Jami’ar Bayero ta Kano da kuma Jami’ar Legas.
Wani makusancin iyalan Farfesa Umar Shehu ya ce Allah Ya yi masa rasuwa ne a ranar Litinin inda ya wallafa cewa, “A madadin al’ummar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, ina sanar da rasuwar dattijo, kaka kuma uban al’umma Farfesa Emiritus Umaru Shehu.
“Za a yi da jana’izarsa da misalin karfe 4.30 na yamma.”
Gidauniyar Raya Al’adu da Tarihin Masarautar (KBHCF) da kuma Kungiyar Dattawan Borno (BEF) ta hannun Dokta Bulama Mali Gubio, sun mika ta’aziyyarsu game da rasuwar.
“Allah Ya jikan babban farfesanmu na fannin kula da lafiyar al’ummar, Umaru Shehu wanda tuna ta san da zamansa a fannin likitanci, wanda ya rasu yana da shekaru 97,” in ji sanarwar tasu.
Takaitaccen tarihin Farfesa Umaru Shehu
An haifi Umaru Shehu ne a a Maiduguri, Jihar Borno, inda ya yi karatun firamare (1935-140) da makarantar middle (1941-1943) sannan ya tafi Kwalejin Kaduna (1944-1947).
Daga nan ya tafi Jami’ar Ibadan, (1948-1953); Jami’ar Liverpool da ke kasar Birtaniya (1953-1956) da kuma 1966-1967).
Ya kammala digirinsa na farko a fannin likitanci a Jami’ar London, inda ya zama mamba a cibiyar binciken cutar kansa kuma Babban Editan Mujallar Likitanci ta Birtaniya.