Bayan Sallar La’asar za a yi jana’izar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh
Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa yana da shekara 82
Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa.
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya.
Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Sudais, sun gabatar da ta’aziyyar iyalai da ɗaliban mashahurin malamin.
Za a gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh bayan Sallar La’asar.
Kazalika za a yi masa Salatul Ga’iba a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina.