Sheikh Adam Tula: Malamin da ba a taba irin jana’izarsa ba a Habasha
Jana’izar wani shehun malamin Islama a yankin Oromo ya kasar Habasha ta tara jama’ar da ba taba ganin ta ba a kasar. Shehun Malamin mai suna Sheikh Adam Tula Al Oromi ya rasu ne yankin na Oromo mai yawan Musulmi a ranar Laraba. Habasha da Eritrea sun kaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen Tigray […]
Jana’izar wani shehun malamin Islama a yankin Oromo ya kasar Habasha ta tara jama’ar da ba taba ganin ta ba a kasar.
Shehun Malamin mai suna Sheikh Adam Tula Al Oromi ya rasu ne yankin na Oromo mai yawan Musulmi a ranar Laraba.
- Habasha da Eritrea sun kaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen Tigray
- Rikicin Tigray: An janye dokar ta-baci a Habasha
An kuma yi jana’izarsa, wadda dubban mutane daga ko’ina suka halarta a kasar — wanda ba a taba ganin taron jana’izar da jama’a suka yi cikar kwari kamarsa ba.
An yi ikirarin cewa malamin ya kai kimanin shekaro 110 a duniya, a inda ya kwashe wadannan shrekarun wajen koyo da koyar da addinin Musulunci a bisa tafarkin Sunna.
“Malamin ya yi fice wajen yaki da shirka da kaucewa bidi’a irin ta gargajiyar kabilar Oruma,” a cewar wani sakon Twitter na wani Yusuf da ya fito daga yankin, wanda kuma ya san malamin.
Musulman kasar na ta kewar sa da kuma addu’ar Allah Ya musanya musu shi da wani mai akida irin tasa.
Hakazalika dailiban malamin da sauran al’ummar Musulmi na ci gaba da bayyana ta’aziyyarsu ga iyalan mashahurin malamin bisa wannan babban rashi.