Sheikh Adam Tula: Malamin da ya shekara 80 yana karantarwa

Sheikh Adam Tula, fitaccen ahehin malamin Musulunci da ya shafe shekaru 80 yana karantarwana kasar Habasha, ya rasu yana da shekaru 110 da haihuwa. Sanarwar rasuwarsa ta bulla ne ta shafin Dokta Muhamed Salah na Facebook, bayan ya shafe shekaru 80 yana karantar da litattafan addinin Islama daban-daban. An rantsar da sabon shugaban mulkin soja […]

Sheikh Adam Tula: Malamin da ya shekara 80 yana karantarwa

Margayi Sheikh Adam Tula

Sheikh Adam Tula, fitaccen ahehin malamin Musulunci da ya shafe shekaru 80 yana karantarwana kasar Habasha, ya rasu yana da shekaru 110 da haihuwa.

Sanarwar rasuwarsa ta bulla ne ta shafin Dokta Muhamed Salah na Facebook, bayan ya shafe shekaru 80 yana karantar da litattafan addinin Islama daban-daban.

Kungiyar Wayar da Kai Kan Shugabanci ta Kabilar Oroma (OLLAA) da margayin ke koyarwa karkashinta, ita ma ta fitar da makamanciyar sanarwar shafinta na Twitter, inda dalibansa da sauran al’ummar kasar suka yi masa addu’ar samun rahama.

Duk da har yanzu ba a bayyana musabbabin rasuwarsa ba a hukumance, rahotanni na nuna lafiya kalau ya rasu.

Shehin malamin dai ya yi fice  wajen karantar da Alkur’ani, da Hadisi ga al’ummar Habashan.

Haka zalika karkashin kungiyar OLLAA da yake karantarwa, suna wayar da kan al’ummar kabilar Oromo da tafi kowacce yawan al’mma a Habashan kan al’amuran kasar, hadi da sauran ’yan kasar da aka danne wa hakki.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos