Sheikh Al Arifi na Saudiyya ya bukaci mawakiya Ahlam ta zama mai wa’azi
Wani malamin addinin Musulunci a Saudiyya ya samu yabo da suka kan kiran da ya yi wa wata mawakiya, ta daina waka ta koma wa’azi. “Ke mai imani ce kuma kina son Allah,” a cewa Muhammad Al Arifi, a cikin sakon da ya aike a shafinsa na twitter, inda ya yi magana da tauraruwa mawakan […]
Wani malamin addinin Musulunci a Saudiyya ya samu yabo da suka kan kiran da ya yi wa wata mawakiya, ta daina waka ta koma wa’azi. “Ke mai imani ce kuma kina son Allah,” a cewa Muhammad Al Arifi, a cikin sakon da ya aike a shafinsa na twitter, inda ya yi magana da tauraruwa mawakan Hadaddiyar Daular Larabawa, Ahlam. “Me zai hana ki sauya rayuwarki tunda Ramadan ya karato, ki zama Ahlam mai wa’azi, amma ba Ahlam mawakiya ba?” kamar yadda ya bijiro mata da tambaya a sakonsa.
Da take mayar masa da amsa, Ahlam, wadda alkali ce a shirin gwarazan ’yan wasa da mawaka na Arab Idol da ake nunawa a tauraron dan Adam, ta ce masa: Allah Ya albarkaceka. Ka yi mana addu’a, Shaikh Muhammad Al Arifi. Muna rokon Allah ya karbi kyawawan ayyukanmu.” Wannan musayar sakonni da suka yi ta haifar da takaddama da muhawara mai zafi, a daukacin fadin yankin tekun Fasha, inda malamin da mawakiyar ke da dimbin magoya baya.
“Ina kaunar Al Arifi saboda jajircewarsa da kwazonsa. Don shi mutum ne wanda ya samu nasara a rayuwa, kyuma da wuya a samu mutum kamarsa, wanda ya jajirce wajen aikin Allah,” inji Abul Hasanain, wani mai baza sakonni ta shafin intanet.
Shi kuwa wani mai baza sakonnin, mai suna Kalima, suka ya yi ga Al Arifi, inda ya ce: “Ban yaba da abin da irin wadannan mutanen ke yi ba, kuma ina shawartar Al Arifi da ya daina kwadayin kambama kansa ta kafar yada labarai, don neman shahara,” domin yana ganin yana cikin mutanen da ke amfanin da kafar sadarwa don daga darajar kansu, kamar yadda yake kunshe a sakon da Kalima ya aike wa Jaridar kasar Kuwait ta Al Watan.