Sheikh Alhassan Sa’eed ya bukaci sababbin shugabanni su yi wa jama’a adalci
Wani fitattacen malamin addinin Musulunci da ke Jos a Jihar Filato, kuma jigo a kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos ya bukaci sababbin shugabanni, su yi wa jama’ar kasar nan adalci kan amanar da aka damka musu. Sheikh Alhassan Sa’eed Adam ya yi wannan kiran ne a […]
Wani fitattacen malamin addinin Musulunci da ke Jos a Jihar Filato, kuma jigo a kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos ya bukaci sababbin shugabanni, su yi wa jama’ar kasar nan adalci kan amanar da aka damka musu.
Sheikh Alhassan Sa’eed Adam ya yi wannan kiran ne a wajen tafsirin watan azumin Ramadan da yake gabatarwa a garin Jos, inda ya ce “Shugabannin da suka gabata ba mu daidaita da su ba, saboda rashin adalcin da suka yi mana. Saboda haka ku sababbin shugabanni, ku yi mana adalci domin ku tafi lafiya da al’ummar Najeriya, al’ummar Najeriya suna yi muku kyakyawan zato.”
Har ila yau ya yi kira ga al’ummar kasar nan su yi wa sababbin shugabannin addu’ar Allah Ya sa su yi wa al’ummar kasar nan ayyuka na alheri.
Sheikh Alhassan Sa’eed ya yi kira ga malamai su ji tsaron Allah su hada kan al’umma a wuraren da suke gabatar da tafsirin azumin watan Ramadan da suke yi a halin yanzu. “Malamai mu hada kai mu ji tsaron Allah a wannan wata, mu guji raba kawunan jama’a. Mu tsayar da mutane kan doron abin da Allah da ManzonSa suka ce. Kada mu kirkiro abin da Allah da ManzonSa ba su ce a yi ba. Duk inda aka samu rarrabuwa ba za a samu zaman lafiya ba, kuma ba za a cimma nasara ba. Musulmi dukkanmu abu guda muke,” inji shi.
Ya yi kira ga iyaye kan a hadu a tarbiyartar da ’ya’ya domin su samu tarbiyya tagari. Ya ce a daina dora wa ’yan mata tallace-tallace domin tallace-tallace na lalata ’ya’ya mata, maimakon haka iyaye su sa yara a makarantun addini da na boko.