Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar da Idin Karamar Sallah
Tijjani Dahiru Bauchi ne ya jagoranci sallar Idi yayin da mahaifinsa ya kasance cikin mamu.
Bajimin Malamin nan na darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman, ya gudanar da Idin karamar Sallah tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba.
Malamin ya gudanar da sallar Idin ne a gidansa da ke birnin Bauchi kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito.
- Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono
- Badakar Naira Biliyan 165: PDP ta bukaci Buhari ya tsige Ministan Sufuri
- Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci Majalisa ta tsige Buhari
Wani dan malamin, Tijjani Dahiru Bauchi ne ya jagorancin sallar Idi yayin da mahaifinsa ya kasance cikin mamu.
A jawabin da Sheikh Dahiru Bauchi ya gabatar bayan idar da sallar Idin, ya ce sun yi sallarsu ne ta Idi saboda sun samu tabbacin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Talata.
Ya ce, “Dangane da wannan labarai na cewa wata ya tabbatar, abin da aka ce adalai guda biyu idan sun gani ya isar ma jama’a, ko kuma jama’a masu yawa idan sun ga watan.
“An ga wata a wurare irin su Gombe da Gadau da kuma Kebbi,” a cewar Malamin.
A cewarsa, ba shi da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin watan, “saboda suna da yawa.
“Shi ya sa yanzu muka zo muka gudanar da sallar Idi domin watan Ramadana ya kare, watan Shawwal ya shigo,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ba da sanarwar rashin ganin watan Shawwal a yammacin ranar Talata, 29 ga watan Ramadan.
Sultan na Sakkwato ya bayyana hakan ne cikin wata takarda da aka raba wa manema labarai a fadarsa da ke birnin Shehu.
Takardar da ke dauke da sa hannun mai baiwa fadar shawara kan harkokin addini kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya ce a duk fadin Najeriya ba a samu labarin ganin watan Shawwal ba, saboda haka Ramadanan bana zai cika kwanaki 30.