Sheikh dahiru Bauchi ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta nuna misali wajen bin doka
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen koya wa mutane yadda za su kiyaye doka, ba ta rika nuna musu yadda za su rika karya doka ko tayar da husuma a cikin kasa ba.Shehun Malamin ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da manema labarai a […]

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen koya wa mutane yadda za su kiyaye doka, ba ta rika nuna musu yadda za su rika karya doka ko tayar da husuma a cikin kasa ba.
Shehun Malamin ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da manema labarai a Bauchi, lokacin da ya mika ta’aziyya kan rasuwar Sarkin Kano tare da nuna rashin jin dadi kan abubuwan da suka wakana kafin aka bar sabon Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II ya shiga fada a matsayinsa na sabon Sarki.
Ya ce hakkin gwamnatin Kano ce ta nada Sarki a Kano ba Gwamnatin Tarayya ba. Don haka ya ce hakkin gwamnati ne ta kwantar da husuma ba tayar da ita ba, musamman ganin yadda ba domin Allah Ya gyara ba komai na iya faruwa a yayin da aka samu matsala game da hana Sarkin shiga fada.
Sheikh dahiru Bauchi ya yaba wa marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero kan ayyuka masu kyau da ya gudanar na bude makarantu da masallatai a jihar, kuma ya yi fatar Allah Ya yafe masa kura-kuransa.
Daga nan ya yi fata Allah Ya Sarki Muhammadu Sanusi sa’ar kama mulki cikin nasara tare da tsawon rai kamar na wanda ya gada.
Ya yaba kan kwanciyar hankalin da aka samu a Kano, inda ya yi addu’ar Allah Ya kawo kwanciyar hankali mai dorewa tare da maganin wadanda suka haifar da fitinar.
Ya bukaci kowane Musulmi musamman ’yan Tijjaniyya su karanta Hasbunallahu 1350 da Salatil Fatih 1111 da Astagfirullahi 1111 da Yaladifu 129 da Lakad Ja’akum 66 da nufin Allah Ya kawo zaman lafiya a kasar nan kuma Ya mayar wa dukkan masu nufin Musulmi da sharri ya koma kansu.
Ya nuna bacin ransa kan yadda aka rufe filin jirgin Kano lokacin dambarwar nadin Sarkin Kano, ya ce shugabannin da ke haifar da hakan ba sa jin maganar malamai, don haka malamai suke fada wa Allah Wanda Shi ne ke amsa maganarsu da addu’arsu.