Sheikh Dahiru ga Obama da Sarauniyar Ingila: Ku dawo Musulunci addinin kakanninku
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira da babbar murya ga tsohon Shugaban Amurka Mista Barrack Obama da Sarauniyar Ingila Elizabeth da sauran Kiristoci su dawo addininsu na Musulunci. Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan kira ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake zantawa da […]
Sheikh Xahiru Usman Bauchi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira da babbar murya ga tsohon Shugaban Amurka Mista Barrack Obama da Sarauniyar Ingila Elizabeth da sauran Kiristoci su dawo addininsu na Musulunci.
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan kira ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Bauchi, don mika sakon ban-gajiya ga mahalarta Mauludin bana.
Ya ce “Ina kira ga Barrack Obama, tsohon Shugaban Kasar Amurka ya duba girman Allah ya dawo addinin kakanninsa, ya kuma duba irin baiwar da Allah Ya yi masa a ce kasa kamar Amurka yana dan asalin Afirka Allah Ya ba shi mulkinta ba don wayonsa ko wata dabara tasa ba, kuma ya gama lami lafiya cikin amincewar Allah.Ga wani ko shekara hudu bai yi ba ana kokarin tsige shi. Dukkan ’yan uwanka Musulmi ne kuma wannan abu da Allah Ya yi maka ya kamata ka dawo ka bauta maSa, za mu yi matukar farin ciki idan muka gan ka a addini na jinkai da zaman lafiya.”
Sheikh ya kara kira da babbar murya cewa “Ku yi wa Allah ku isar min ga Sarauniyar Ingila “Kueen Elizabeth” ta dubi girman Allah ta dawo addinin kakanninta. Sheihin ya ce “Allah Ya yi miki tarin baiwa kin mulki kasar Ingila tun kina karama, shekara sama da 60 kina mulki, kin more matukar morewa a wannan duniya. Babu babbar arziki da za ki kara morewa a Lahira fiye da morewarki ta duniya kamar wannan addini na Musulunci.”
Sheikh Dahiru Bauchi ya kammala da cewa, “Muna roka musu Allah Ya yi musu arziki da wannan addini da Manzon Allah (SAW) ya zo mana da shi.”