Sheikh Daurawa ya yi murabus daga shugabancin Hisba

Malamin ya sanar da murabus dinsa ne a cikin wani bidiyo, inda ya ce gwiwarsa ta yi sanyi da jin suka da gwamnan Kano ya yi kan yadda Hisbah ke gudanar da ayyukanta a jihar Kano

Sheikh Daurawa ya yi murabus daga shugabancin Hisba

Sheikh Muhammad Amin Ibrahim Daurawa

Shugaban Hukumar Hisba na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi murabus da mukaminsa.

Daurawa ya sanar da saukarsa daga shugabancin hukumar ne bayan kalaman gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya yi na sukar yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta na yaki da badala a jihar.

Daurawa, ya sanar da murabus dinsa daga shugabancin hukumar, a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar ranar Juma’a.

Kalaman gwamna Abba Gida-Gida, sun yamutsa hazo a jihar, inda wasu ke ganin kalaman nasa a matsayin wata gaba ta goyon bayan masu aikata badala a jihar.

Bayan kalaman gwamnan jihar, mutane da dama sun yi ta kiraye-kirayen neman shahararren malamin ya sauka daga shugabancin hukumar domin tsira da mutuncinsa.

Idan ba a manta ba hukumar Hisba a jihar ta fito da sabon salon yaki da baɗala, inda ta dinga kai samame wurare shakatawa da otal-otal tana  kama masu yawon ta-zubar.

A baya-bayan nan, Hisba ta cafke fitacciyar ’yar TikTok Murja Ibrahim Kunya, tare da gurfanar da ita a gaban kotu, wanda hakan ya sa aka tasa keyarta zuwa gidan yari.

Daga bisani Murja ta yi layar bata daga gidan yari, lamarin da ya tayar da kura da haifar da cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta.

Lamarin dai ya sanya wasu na ganin matashiyar na da uwa a gindin murhu a gwamnatin jihar mai ci, duba da irin gudunmawar da ta bayar wajen kafuwar gwamnatin.

Sai dai gwamnatin jihar a wani martani da ta yi, ta hannun Kwamishinan Yada Labaran jihar, Baba Dantiye, ya musanta wannan zargi da ake yi wa gwamnatin.

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025