Sheikh Dokta Yusuf Ali ya rasu

Yau da Azahar za a yi jana’izar fitaccen malamin Musulunci a Kano, Sheikh Dokta Yusuf Ali, a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo

Sheikh Dokta Yusuf Ali ya rasu

Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kano, Shaikh Dokta Yusuf Ali rasuwa.

Sheikh Dokta Yusuf wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya ya rasu ne a daren Lahadi bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 73.

Yar marigayin, Dokta Bilkisu Yusuf Ali ta shaidawa Aminiya cewa za a yi janaizarsa a yau Litinin da Azabar a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo.

Shehin malamin ya gudanar da rayuwarsa ta aikin gwamnati a matsayin alkali, inda ya jagorancin kotunan Shari’ar Musulunci daban-daban a Jihar Kano, kafin ya yi ritaya a shekarar 2009.

Bayan koyarwar addinin da ya dauki tsawon lokaci yana yi, malamin ya yi tashe wajen taimaka wa al’umma ta bangaren neman lafiya daga shafar aljanu.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024