Sheikh El-Miskin ya rasu yana da shekara 115
Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Maiduguri, Sheikh Abubakar El-Miskin rasuwa. Malamin wanda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata yana da shekara 115, daruruwan malaman addini da suka fito daga jihohin Borno da Yobe da sauran sassan Najeriya da kuma kasashen Nijar da Kamaru da Chadi ne suka […]
Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Maiduguri, Sheikh Abubakar El-Miskin rasuwa.
Malamin wanda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata yana da shekara 115, daruruwan malaman addini da suka fito daga jihohin Borno da Yobe da sauran sassan Najeriya da kuma kasashen Nijar da Kamaru da Chadi ne suka kasance almajiransa. An yi jana’izarsa a washegari a garin Maiduguri inda dubban jama’a ciki har da manyan jami’an gwamnatin Jihar Borno da manyan mutane daga ciki da wajen jihar suka halarta. Marigayi Sheikh El- Miskin ya rasu ya bar mata da iyaye 31 da ’ya’ya 240 da kuma dimbin tattaba kunne. Daga ’ya’yansa akwai Farfesa Tijjani El-Miskin.