Sheikh Gumi ga Jonathan da Buhari: Ku hakura da takara
Ffitaccen malamin addinnin Musuluncin nan da ke Kaduna, Dokta Ahmad Abubakar Gumi ya nemi tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da kada ya tsaya takarar Shugaban kasa a zaben badi, inda ya bukaci Jam’iyyar PDP ta canja Jonathan a matsayin dan takararta domin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan. Dokta Ahmad Gumi ya bayyana […]
Ffitaccen malamin addinnin Musuluncin nan da ke Kaduna, Dokta Ahmad Abubakar Gumi ya nemi tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da kada ya tsaya takarar Shugaban kasa a zaben badi, inda ya bukaci Jam’iyyar PDP ta canja Jonathan a matsayin dan takararta domin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.
Dokta Ahmad Gumi ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa Janar Buhari ta shafinsa na Twitter, inda ya ce, ’yan siyasa na amfani da Janar Buhari ne kawai domin su cimma burinsu na siyasa saboda farin-jinin Janar din a tsakanin talakawan kasar nan.
Wannan wasika ta zo ne bayan mako daya da Janar Buhari ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC.
Ya fadi a wasikar cewa, rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne manyan bala’o’in da kasar nan take fuskanta tun samu mulkin kai. Ya shaida masa cewa yunkrinsa na yaki da cin hanci da rashawa ba shi ne mafi muhimmanci ga Najeriya ba a yanzu “Abin da Najeriya take bukata a yanzu shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali,” inji shi.
Ya ce, “A yanzu Najeriya tana neman zaman lafiya da kwanciyar hankali tukunna. Sannan mu yi maganar kyakkyawan shugabanci duk da cewa rashinsa ne ya jefa mu a bala’in da muke ciki.”
Dokta Gumi ya ce, “Gwamnati mai ci ta riga ta canja al’amura, ta yi amfani da addini ta raba kan jama’a domin ta cimma burinta. Wani fasto daga Yamma maso Kudu har kiran Kiristoci da coci yake yi cewa su zabi Jonathan a matsayin mai cetonsu. Da addini ake amfani yanzu wajen rufe gazawarsa a bangaren mulki.”
Ya kara da cewa, “Mai girma, ya kamata kai ma ka sani cewa da dama ko mafi yawan magoya bayanka suna fata ne ka kare su daga cin zarafin addininsu da yankinsu da ake yi. Haka Kirista ba yake kallo. Don haka an shata daga ta fafatawa a tsakanin mabiya addinai, wanda ba shi kasar take bukata ba. Abin da muke bukata shin ne zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Duk da dai Dokta Gumi ya fi bayani kan Janar Buhari, ya kuma bukaci Shugaba Goodluck Jonathan da kada ya tsaya takarar a zaben na 2015 domin a samu zaman lafiya a kasar nan.
Dokta Gumi ya ce, idan Jonathan ya sake hawa kujerar mulkin kasar nan, nan ne za a ga hakikanin Boko Haram ba ta siyasa da muke gani a yanzu ba. “Tashin hankali zai mamaye daukacin kasar nan ba Arewa kadai ba. Don haka ina kira ga Jam’iyyar PDP ta gabatar da wasu ’yan takara maimakon Jonathan.”
Wakilinmu ya tuntubi Sheikh Ahmad Gumi dangane da dalilinsa na yin kira ga Shugaba Jonathan da Janar Buhari su janye takararsu ta neman kujerar shugabancin kasar nan a shekarar 2015, ya amsa kamar haka:
Ka bukaci Shugaban kasa Jonathan da Janar Buhari su hakura su janye daga takarar shugabancin kasar nan ko kana da dalilin kiran?
Sheikh Gumi: Abin da ya sa na yi wannan kira shi ne, in ka tuna kimanin shekaru biyu ko uku da suka wuce akwai wata ma’aikata ko jami’a a Amurka da ta yi rubutu cewa Najeriya za ta wargaje a shekara ta 2015. To mutumin da ke wajen kasa ma, ba na cikinta ba, ya hango yadda muke tafiya da al’amari, za mu wargaje. An yi kokarin a raba Najeriya da taron tattaunawa na kasa da ya wuce, abu ya buwaya. An dauko yakin kariya, aka gane dai duk shirme ne, aka rarraba sojoji…
Wadannan mutane biyu sun yi takara a da kuma ka ga abin da ya faru. Yanzu ana ta yin duk abin da ake iyawa don su sake tsayawa takarar tare. Ana ta jin maganganu iri-iri na abin da zai auku idan dayansu ya fadi a zabe. Misali idan Shugaba Jonathan ya fadi, akwai wadanda ba za su yarda, su hakura ba. Haka nan idan Janar Buhari ya fadi, talakawa, wadanda mafi yawansu ba su san kowa ba, sai shi, ba za su yarda ba. Saboda haka nake cewa kowanensu ya dubi Allah, ya ga cewa don su biyu kawai, bai kamata a yi sanadin rasa miliyoyin rayuka ba. Shi ya sa na ce su hakura da takarar, jam’iyyunsu su dauko wadansu daban su tsayar da su ta yadda in kowanensu ya fadi, ba wanda zai ce bai yarda ba, balle a samu wani tashin hankali a kasa.
Ba ka ganin wannan kira zai iya jaza wa Arewa wani cikas?
Sheikh Gumi: Ai abin ba na bangaranci ba ne. Idan ka tuna baya, a tarihi, Awolowo ya yi fafutukar shugabancin kasar nan, amma Yarabawa ne kawai ke son shi. Yana da kyakkyawan tsari, wanda ya ce kowa zai samu ilimi kyauta, misali, amma a haka ya hakura. Ojukwu ya yi wa Ibo aiki, suna sonsa, amma ai ka ga inda ya ja su, suka fada! Saboda haka su ma wadannan shugabanni namu, wato Goodluck da Buhari, kowanensu yana da bangaren da ke goyon bayansa, wanda kamar yadda na ce, wanda duk ya fadi a cikinsu, ba za a hakura a tafi a haka ba.
To, kana da wani dan takara da kake ganin ya cancanta a tsayar da shi?
Sheikh Gumi:A’a, ai kowane dan siyasa yana da fuska biyu; ta siyasa, wadda jama’a suke kallonsa da ita, sai kuma tashi ta asali, wato halinsa na mutumtaka. Abin da dai nake bukata shi ne kasa ta zauna lafiya kowa ya yi addininsa ba tare da tsangwama ba.
Abin da nake gani shi ne kowace jam’iyya ta samu matasan ’yan siyasa, masu jini a jika, wadanda suke karbabbu ga jama’a, a tsayar da su, ta yadda in kowanensu ya fadi, ba wani tashin hankali da ake ganin zai faru.
Amma a gaskiya tun kafin a yi nisa, wannan takara ta Shugaba Jonathan da Janar Buhari, akwai bukatar a yi kira gare su da su janye ta, su ba da wuri, don a guje wa abin da ake hasashen zai auku na tashin hankali a kasar nan.
Sai dai wani kira da nake son in yi wa mutanenmu, musamman na nan Arewa, tun ma dai ba musulmi ba, an bar mu a baya sosai, ta fannin ilimi, tattalin arzikin kasa. Hanyoyi dai da yawa, an bar mu a baya. Saboda haka wannan jahilcin da ya shafi al’umma, ba wuya za a iya amfani da shi a kawo rikici a kasa, musamman a bangarenmu, ta yadda za a samu dama a fito da sojoji da jami’an tsaro, a yi mana abin da aka saba, idan an samu irin wannan tarzoma. Shi ya sa nake ganin ya kamata mu yi wa kawunanmu fada, cikin hankali da hikima da tsanaki, kada mu yarda, ko yaya, a tada hankali a cikin wannan zabe. Mu daure, mu yi hakuri. Idan an bi abubuwa haka da hikima, to shi ke nan, karshe dai za a samu nasara.