Sheikh Tijjani Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗi da kayan abinci
Kusan duk mutanen da suka halarci majalisin malamin a daren ranar Litinin sun samu wannan kyauta
Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Tijjani Yusuf Guruntum, ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗade da kayan abinci.
Sheikh Tijjani Guruntum ya raba wa daliban nasa wannan kwanakin arziki ne bayan kammala karatu a ranar Litinin.
Daya daga cikin daliban malamin mai suna Muhammad Sagir Ibrahim, ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna cewa kusan duk ɗaliban da suka halarci majalisin malamin a na ranar Litinin bayan sallar isha’i ya samu wannan kyauta.
Wata majiya ta bayyana cewa malamin ya yi rabon ne ga ɗalibai sama da 50 da suka halarci majalisin.
- HOTUNA: Yadda aka naɗa Hadimar Al-Kur’ani Mace ta Farko a Zariya
- Matatar Dangote: Minista na neman sasanta NNPC da Dangote
Rahoton da Aminiya ta samu ya nuna wasu sun samu kwalin taliya da kuɗi, wasu sun samu kuɗi Naira dubu 10, wasu kuma dubu 20, wasu kuma 30 har da waɗan da suka samu sama da haka.
“Wannan fa zallar [kyautar] ɗalibai ce aka yi yau.
“Za a yi na mutanen gari [daga bi sani] inda aka tanadi shinkafa da gero da sauran kayan abinci da za a raba wa mutanen gari cikin wannan satin in sha Allahu,” a cewar majiyar.