Sheikh Ibrahim Khalil ya zama dan takarar Gwamnan Kano a ADC
Shi ne dai zai yi wa jam’iyyar takara a zaben 2023 mai zuwa a Jihar
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya zama dan takarar Gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar ADC.
Ya sayi fom din takarar ne kan Naira miliyan 10 sannan zai zama dan takarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa kasancewar shi kadai ne ya sayi fom din kujerar.
- Dan takarar da ke hannun ’yan bindiga ya lashe zaben fid da gwanin PDP a Kaduna
- Shin da gaske ne Dangote na fama da karayar arziki?
A cewar Shugaban jam’iyyar ta ADC a Jihar Kano, Musa Shu’aibu Ungogo, shugabannin jam’iyyar ne da kan su suka yanke shawarar zuwa har Jihar Kano don kawo masa fom din saboda muhimmancinsa da na Jihar.
Ya ce, “Dukkan sauran masu neman takara sukan je hedkwatar jam’iyyar ne a Abuja don sayen fom, amma shi Sheikh Khalil bayan ya biya kudin, sai suka ce ya dawo za su kawo masa har gida.
“Hakan ne ya sa Shugaban jam’iyyar na kasa da Sakatarensa da kuma Mataimakin Shugaba na Shiyyar Arewa maso Yamma suka zo har Kano don gabatar masa da fom din.
“Shugaban ya kuma yi amfani da bikin wajen rantsar da Shugabannin shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar, karkashin Farfesa Kabiru Dandago.
Ya ce ya zuwa yanzu, shehin malamin ne kawai ya sayi fom din takarar Gwamnan a Jihar.
Shugaban jam’iyyar ya kuma yi kira ga mutanen Jihar da su yi watsi da jam’iyun APC da PDP saboda ya ce su ne suka kashe Najeriya, inda ya ce ADC ta sha bamban da su.
Idan za a iya tunawa, a watannin baya ne dai Sheikh Ibrahim Khalil ya sanar da ficewarsa daga APC sannan daga bisani ya koma ADC.
A zabukan baya, ya taba neman takarar kujerar a jam’iyyar APC, amma bai yi nasara a zaɓen fid da gwani ba.