Sheikh Jingir ga Obasanjo: Ba ka da bakin da za ka ce kada Buhari ya sake tsayawa takara
Shugaban Majalisar Malamai ta Qungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Qasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce wasiqar da tsohon Shugaban Qasa Olusegun Obasanjo ya rubuta cewa kada Shugaba Buhari ya sake tsayawa takara a zaben badi magana ce da ba ta dace ba. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne […]
Shugaban Majalisar Malamai ta Qungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Qasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce wasiqar da tsohon Shugaban Qasa Olusegun Obasanjo ya rubuta cewa kada Shugaba Buhari ya sake tsayawa takara a zaben badi magana ce da ba ta dace ba.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da nasiha a Masallacin Juma’a na ’Yan-taya da ke garin Jos, inda ya ce Allah ne Ya bai wa Buhari mulkin Najeriya ba don wayo ko kudi ba, saboda babu yadda ba a yi ba, domin ganin bai ka nasara ba, amma Allah Ya ba shi mulkin.
Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa Shugaba Muhammadu Buhari damar sake tsayawa takarar shugabancin qasar nan a karo na biyu.
Sheikh Jingir ya yi bayanin cewa a lokacin mulkin Obasanjo, bayan ya cika wa’adinsa karo na biyu, ya yi qoqarin ya karya kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tazarce karo na uku da qarfi.
“Mutumin da ya so ya karya kundin tsarin mulkin Najeriya, bayan ya yi shekara 8 yana mulki ya so ya yi tazarce da qarfi yana da bakin da zai yi maganar cewa kada Buhari ya sake tsayawa takarar shugabancin qasar nan? An yi wa Buhari adalci a ce kada ya qara tsayawa takara, bayan ya yi shekara 4, bayan kuma tsarin mulki ya ba shi damar ya sake yin shekara 4? Wanda yake cewa kada ya sake tsayawa, bayan shi ya yi shekara 8 fa ya yi qoqarin ya yi tazarce karo na uku.”
Sheikh Jingir ya ce Obasanjo ne ya fara bata Majalisar Dokoki ta Qasa ta hanyar ba majalisun biyu cin hanci da rashawa. Don haka ba ya da bakin da zai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawarar cewa kada ya sake tsayawa takara a zaben badi.
Ya ce a lokacin gwamnatin da ta gabata an so a hallaka Arewa baki daya ta hanyar kashe mutanenmu a kullum. Don haka mutanen Arewa baki daya Musulmi da Kirista, suka fito suka zabi Shugaban Qasa Muhammadu Buhari.
Sheikh Jingir ya ce “A Najeriya ban taba ganin Shugaban Qasar da azalumai suka dawo da kudaden da suka sace kamar wannan lokaci na Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ba. Buhari ya yi qoqari wajen rusa ’yan Boko Haram da suka addabi al’ummar Arewacin Najeriya, a zamanin gwamnatin da ta gabata.”
Sheikh Jingir ya ce “Muna goyon bayan Buhari saboda ba ya cikin barayin da suka lalata Najeriya, kuma muna goyon bayan Buhari saboda ba ya cikin ashararan shugabannin Najeriya.”