Sheikh Jingir ya bukaci a sassauta dokar ta-bacin da aka kafa
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Badi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya yi kira ga mahukuntan Najeriya su sassauta dokar ta-bacin da suka sanya a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, domin a ceto al’ummar jihohin daga mawuyacin halin da suka shiga saboda kafa dokar. Sheikh Sani Yahya […]

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Badi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya yi kira ga mahukuntan Najeriya su sassauta dokar ta-bacin da suka sanya a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, domin a ceto al’ummar jihohin daga mawuyacin halin da suka shiga saboda kafa dokar.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi kiran ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, inda ya ce dokar tana matukar cutar da al’ummomin da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohin, inda dukkan harkokin kasuwanci da na al’amuran yau da kullum suka tsaya ciki.
Ya yi kira ga shugabannin Najeriya da shugabannin addinai da sauran al’umma kan kowa ya ba da gudunmawarsa wajen ganin an gina zaman lafiya da kwanciyar hankali da c igaba a kasar.Ya ce halin da ake ciki Najeriya tana bukatar addu’a don a samu dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.