Sheikh Jingir ya bukaci Buhari ya farfado da ilimi
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari da zarar an rantsar da shi, ya yi kokari wajen sake farfado da harkokin ilimi a kasar nan. Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne […]
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari da zarar an rantsar da shi, ya yi kokari wajen sake farfado da harkokin ilimi a kasar nan.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe gasar karatun Alkur’ani Mai girma karo na 18 da reshen kungiyar na karamar Hukumar Jos ta Arewa ya gudanar a garin Jos.
Ya ce ya zama wajibi Janar Buhari ya tashi tsaye wajen ceto harkokin ilimi daga durkushewar da ya yi, saboda babu abin da ya kai ilimin muhimmanci a rayuwar al’umma. Kuma ya yi kira ga Janar Buhari ya zabi mutane nagari wadanda za su taimaka masa a sabuwar gwamnatin da zai kafa.
Sheikh Jingir ya ce neman ilimi wajibi ne a kan al’umma musamman al’ummar Musulmi, inda ya yi kira ga Musulmi su tashi su rungumi karatu da neman ilimi. Kazalika ya yi kira ga Musulmi su rika karanta Alkur’ani Mai girma domin ni’ima tana nan a ciki. “Duk wanda ya yi imani da Alkur’ani ya karanta shi, ya yi aiki da shi zai samu kyakyawar rayuwa.
A jawabin ko-odinetan gasar, Ustaz Ahmad Aliyu ya ce sun samu gagarumar nasara a gasar da aka kammala. Ya ce ’yan takarar da suka shiga gasar su127 sun yi kokari a matakan da suka fafata.
Ya ce wadanda suka zamo na daya da na biyu a gasar, su ne za su wakilci karamar hukuma a gasa ta jihar da za a gudanar nan ba da dadewa ba, sai ya bukace su kara zage damtse da karatu don su samu nasara.