Sheikh Jingir ya bukaci gwamnati da al’umma su kara jan damara wajen yakarsu

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci gwamnati da al’ummar Najeriya su kara jan damara wajen yakar ’yan Boko Haram da ake yi a halin yanzu.  Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi […]

Sheikh Jingir ya bukaci gwamnati da al’umma su kara jan damara wajen yakarsu
Sheikh Jingir ya bukaci gwamnati da al’umma su kara jan damara wajen yakarsu

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci gwamnati da al’ummar Najeriya su kara jan damara wajen yakar ’yan Boko Haram da ake yi a halin yanzu. 

Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi a Masallacin Juma’a na ’Yan Taya da ke garin Jos a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya ce, “wajibi ne mu jama’a da gwamnati mu kara jan darama kan yakar wadannan miyagu, domin karfinsu ya riga ya kare, asirinsu ya riga ya gama tonuwa yanzu babu labarin sun kama garuruwa.”
Sheikh Jingir ya ce “Ana sakaci a kan yadda ake kasa kama wadannan miyagu da suke
kai hare-hare a kasar nan. Ta yaya za a bar wadannan mutane, suna ta kai mana hare-hare ba tare da an kama su ba? Ya kamata a taru a bi wadannan mutane a kama su a yi rugugu da su. Bai kamata mu yi shiru saboda tsoron wadannan mutane masu kashe jama’armu ba, domin wannan tsoro ba zai taimaka mana ba.Ya kamata duk inda aka san akwai ’yan Boko Haram a kai wa jami’an tsaro rahoto.”
Har ila yau ya yi kira ga gwamnati ta sanya na’urorin bincike na tsaro a otal-otal, ta yadda za a rika ganin dukkan mutanen da suke zuwa wuraren.
Ya bukaci a kara tsaurara tsaro a tashoshin mota da kasuwanni da masallatai da coci-coci, don ganin an yi maganin wadannan miyagun mutane da suke kai hare-hare.
Kuma ya yi kira a cigaba da yin addu’ar Allah Ya tona asirin ’yan Boko Haram tare da dukkan masu taimaka musu.