Sheikh Jingir ya bukaci ’yan majalisa su sanya hannu kan kasafin kudin bana
Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukci wakilan Majalisar Dattawa da ta Wakilai su taimaka wa al’ummar Najeriya, su sanya hannu kan kasafin kudin bana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar musu.Sheikh Sani Yahya Jingir ya bukaci haka ne a lokacin […]
Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukci wakilan Majalisar Dattawa da ta Wakilai su taimaka wa al’ummar Najeriya, su sanya hannu kan kasafin kudin bana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar musu.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bukaci haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Jos, inda ya ce duk da suna cewa akwai kura-kurai a cikin kasafin kudin, an yi shekaru da dama ba a yi kasafin kudi kan lokaci, kamar wannan ba, kuma kasafin ya fi na shekarun baya yawa.
“Domin idan ’yan majalisun biyu ba su sanya hannu a kasafin kudin ba, za a wayi gari duk ’yan Najeriya suna jin haushinsu, domin an san Shugaba Buhari ya gabatar musu da kasafin amma sun ki su sanya hannu,” inji shi.
Ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su kara godiya ga Allah kan wannan gwamnati da Ya kawo, domin a bara kamar yanzu ana ta kogin jinin al’umma ana ta kone-konen garuruwa da kauyuka da kasuwanni, “amma Allah Ya fitar da mu daga cikin wannan mawuyacin hali ta hanyar
addu’o’in da muka yi ta yi, Ya kawo mana Shugaba Muhammadu Buhari, don haka mu yi wa Allah godiya wajen mara masa baya har a kai ga nasara,” inji shi.