Sheikh Jingir ya bukaci ’yan siyasa su hada kai kan takarar da suka fito
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil BidI’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga ’yan siyasar kasar nan su hada kai da juna kan takarar da suka fito, don shiga zabe mai zuwa. Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi […]
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil BidI’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga ’yan siyasar kasar nan su hada kai da juna kan takarar da suka fito, don shiga zabe mai zuwa.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1436 da reshen kungiyar ya shirya a garin Jos.
Ya ce bai dace ba kowa ya ce sai ya yi shugabanci, “ya kamata mu san cewa babu wanda zai yi abin da Allah bai ba shi iko ba, don haka ya kamata ’yan siyasa su sasanta a junansu a zabi wadanda suka cancanta don a ceto kasar nan daga halin da ta shiga,” inji shi.
Sheikh Jingir ya ce dukkan ’yan takarar da suka fito a matakai daban-daban ya kamata su san cewa al’ummar Najeriya suna jin jiki, kan abubuwan da suke faruwa.
Sheikh Jingir ya ce kwadayi da ganganci da son kai da kabilanci ne suka kai mu ga halin da muke ciki a kasar nan. Daga nan ya yaba wa kungiyar Izala reshen jihar kan irin ayyukan da take gudanarwa.