Sheikh Jingir ya kalubalanci ’yan boko Fulani kan matsalolin da suke damun Fulani makiyaya
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’iah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya kalubalanci shugabannin al’ummar Fulani su tashi su bada gudunmawa wajen ganin an magance matsalolin da suke damun Fulani a Najeriya. Sheikh Sani Yahya Jingir ya kalubalanci shugabannin al’ummar Fulanin ne a lokacin da yake jawabi a […]
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’iah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya kalubalanci shugabannin al’ummar Fulani su tashi su bada gudunmawa wajen ganin an magance matsalolin da suke damun Fulani a Najeriya.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya kalubalanci shugabannin al’ummar Fulanin ne a lokacin da yake jawabi a wajen bitar da kungiyar ta shirya wa shugabannin al’ummar Fulani a garin Jos, inda ya ce a Najeriya akwai Fulani farfesoshi da masu digirin digirgir, akwai shehunan malaman addinin Musulunci da manyan masu kudi Fulani. Ya ce ina ayyukan da wadannan muhimman mutane suka yi, don magance matsalolin da suke damun al’ummar Fulani a kasar nan?
Ya ce ya kamata manyan shugabanni Fulani masu ilimi su fito da hanyoyin da za a magance matsalolin Fulani. Ita kuma kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta je ta tsara hanyoyin da za a tara kudi don a tunkari matsalolin da suke damun Fulani a Najeriya.
Ya ce ya wajaba al’ummar Fulani su tashi su nemi ilimin addini da na zamani kuma su rungumi kiwo da noma da sana’o’in hannu da kasuwanci da aikin gwamnati.
Har ila yau ya yi kira ga al’ummar Fulani su rika mutunta kansu su daina sanya tufafi marasa kyau.
A jawabin shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa Alhaji Ardo Kiruwa ya yi kira ga Fulani su fahimmci cewa al’ummar Fulani al’umma ce mai mutumci. Ya yi kira ga wadanda suka halarci taron su yi aiki da abubuwan da aka koya masu a wurin taron.
Ya yaba wa kungiyar Izala kan shirya wannan taro, inda ya ce babu taron zai kawo ci gaba ga al’ummar Fulani.
A jawabin shugaban kwamitin shirya taron kuma mataimakin shugaban majalisar gudanarwa na kungiyar Izala ta kasa Ustaz Abdul Nasir Abdul Muhyi ya ce ganin yadda tarbiyyar matasa Fulani take tabarbarewa ne ya sanya Sheikh Sani Yahya Jingir ya umarci kwamitin kula da Fulani makiyaya (Njange Ndure) na kungiyar ya shirya taron bitar, don fadakar da Fulani makiyaya kan muhimancin kula da tarbiyya da halaye masu kyau, saboda a dawo da tarbiyyar da aka san Fulani da ita.
Taron na yini daya ya samu halartar mutum 663 da suka fito daga jihohin Najeriya da
Jamhuriryar Nijar, inda aka gabatar da makaloli uku da suka hada da Biyayya ga Iyaye da Sheikh Sani Yahya Jingir ya gabatar da Kyawawan dabi’u da Sheikh Muhammad Yusuf Sambo Rigachikum ya gabatar da kuma Amana a Musulunci da Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya gabatar.