Sheikh Jingir ya nemi Ganduje da Kwankwaso su kawo karshen rikicinsu

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da magabacinsa Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso su harzarta kawo rikicin da ke tsakaninsu domin amfanin al’ummar jihar.Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa […]

Sheikh Jingir ya nemi Ganduje da Kwankwaso su kawo karshen rikicinsu
Sheikh Jingir ya nemi Ganduje da Kwankwaso su kawo karshen rikicinsu

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da magabacinsa Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso su harzarta kawo rikicin da ke tsakaninsu domin amfanin al’ummar jihar.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jos inda ya nuna takaicinsa kan rikicin siyasar da ke faruwa a tsakanin Gwamnan Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya ce wannan rikicin siyasa da ke faruwa sharri ne na Shaidan, domin shugabannin biyu sun yi shekara takwas suna mulkin Jihar Kano a matsayin Gwamna da Mataimakinsa, kuma sun kawo gagarumin ci gaba a jihar. Don haka ya yi  kira gare su kan su kawar da duk wata matsala da ta taso ta tsakaninsu kuma su ci gaba da zumuncin da aka sansu da shi, domin su ci gaba da kawo abubuwan ci gaba a jihar da Najeriya baki daya Sheikh Jingir ya kuma bukaci jami’an gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari su taimaka masa, domin ya samu nasarar aiwatar da kyawawan kudirorinsa na gyara kasar nan.
Sheikh Jingir ya ce kada wadanda suke cikin gwamnati Buhari su zamanto matsala ga kasar nan, maimakon haka su taru su taimaka masa domin ya samu nasara. Ya ce Shugaban kasa na da kyakyawar manufar raya kasar nan, domin haka a taru a goya masa baya domin ya samu nasara.
Sheikh Jingir ya kuma nuna goyon bayansa ga kiran da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi II ya yi ga Shugaba Buhari, kan ya duba maganar tsare-tsaren tattalin arzikin kasar nan na gwamnatinsa domin ya yi gyara.
Ya ce wannan kira da Sarkin Kano ya yi daidai ne, don haka ya bukaci Shugaba Buhari ya saurari kiran na Mai martaba Sarkin Kano tare da sauran kiraye kiraye irin wadannan..