Sheikh Jingir ya shawarci manoma su daina sayar da kayan abinci ga masu boyewa
Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga manoma su guji sayar da kayan abincin da suka noma ga masu saya suna boyewa don ya yi tsada.
Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga manoma su guji sayar da kayan abincin da suka noma ga masu saya suna boyewa don ya yi tsada.
Shehun Malamin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos babban birnin Jihar Filato a farkon makon nan.
Yana mai cewa, masu sayen abinci su boye don ya yi tsada a yanzu haka sun fitar da makudan kudi don saye abincin da manoma suka noma a bana, saboda irin ribar da suka samu a shekarar da ta gabata.
Sai ya yi kira ga manoma su kiyayi sayar da amfanin gona ga irin wadannan mutane, domin idan farashin kayan amfanin gonar ya tashi za a cuci al’umma saboda wasu da kyar za su iya saye sakamakon tsadarsa ga kuma halin kunci da ake fama da shi a kasar nan.
- Kotu ta rufe aususun Gwamnatin Kano a CBN da sauran bankuna —Lauyan ’yan kasuwa
- Tudun Biri: An fara tattauna biyan diyyar Harin Mauludi
“Manoma ku guji sayar da abincin da kuka noma ga masu boye kayan abinci, mu hakura da yanayin da muke ciki, abincin nan zai yi mana amfani nan gaba, musamman ganin halin da muka shiga na rashin abinci a daminar da ta gabata.
“Mu yi tattali, mu guji yin manyan bukatu, mu adana abincin da muka noma, mu sayar da kadan. Mu guji dora wa kanmu babbar bukata,” in ji shehin malamin.
Sai ya yi gargadi ga masu sayen abincin don boyewa da su ji tsoron Allah. Don Allah ba Ya son wannan abu da suke aikatawa na boye abinci domin ya yi tsada su sayar.