Sheikh Jingir ya soki janye jami’an tsaron Tambuwal

Shugaban Majalisar Malamai ta Qungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Qasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya soki janye jami’an tsaron Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da gwamnati ta yi, inda ya bayyana hakan da karya tsarin mulki da siyasantar da sha’anin tsaron qasar nan. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana […]

Sheikh Jingir ya soki janye jami’an tsaron Tambuwal
Sheikh Jingir ya soki janye jami’an tsaron Tambuwal

Shugaban Majalisar Malamai ta Qungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Qasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya soki janye jami’an tsaron Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da gwamnati ta yi, inda ya bayyana hakan da karya tsarin mulki da siyasantar da sha’anin tsaron qasar nan. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a wajen buxe ofishin qungiyar ’yan sintiri a Unguwar Ali Kazaure da ke garin Jos, inda ya ce idan har a tsarin mulkin qasar nan na 1999, akwai inda aka ce gwamnati ta janye wa mutum jami’an tsaro saboda bambancin siyasa ko addini to a yi gyara a wajen domin kuskure ne. Sheikh Jingir ya ce kowane xan Najeriya yana haqqi a kan gwamnati na ta kare rayuwarsa da dukiyarsa ba tare da lura da bambancin siyasa ko addini ba. Don haka matakin da gwamnati ta xauka na janye wa shugaban majalisar jami’an tsaro babban kuskure ne. Sheikh Jingir ya ce tsaro da zaman lafiya su ne ginshiqan ci gaban kowace al’umma a duniya, don haka ya buqaci gwamnati da al’ummar qasar nan su tallafa wa qungiyar ‘yan sintiri kan aikin da take yi, na tallafa wa wajen samar da tsaro. Taron ya samu halartar wakilan Kwamandan Rundunar Tsaro ta STF da na Hukumar Civil Defence da Hukumar NDLEA da shugabannin addini da ’yan siyasa da sauransu.