Sheikh Maibarga ya mutu a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi a Kebbi
Wani bidiyo da ake zargin masu garkuwar ne suka fitar ya nuna yadda lafiyar Sheikh Maibarga ta taɓarɓare.
Malamin addinin Musulunci na ƙungiyar izala ta JIBWIS, Sheikh Muhammad Maibarga, ya riga mu gidan gaskiya a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi a Ƙaramar Hukumar Koko/Besse ta Jihar Kebbi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman ne ya tabbatar da rasuwar malamin ga manema labarai.
- Gwamnatin Sakkwato ta tallafa wa Alhazai 47 da suka ɓatar da kuɗin guzurinsu
- Wani matashi ya rasu yana tsakar buga ƙwallon ƙafa a Filato
Ya bayyana cewa rundunar ta samu labarin mutuwar malamin yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
“Mun samu rahotannin da suka shafi rashin lafiyarsa da kuma rasuwarsa yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da shi,” in ji kakakin ’yan sandan.
Ana iya tuna cewa dai an yi garkuwa da marigayin malamin addinin tare da wani abokinsa, tsohon shugaban jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Koko/Besse.
Wani bidiyo da ake zargin masu garkuwar ne suka fitar ya nuna yadda lafiyar Sheikh Maibarga ta taɓarɓare kafin daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
Wani makusancin iyalansa, Usman Aliyu, ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin ceto shi daga hannun masu garkuwar lokacin da ya rasu sakamakon matsananciyar rashin lafiya.
Ya bayyana cewa har zuwa lokacin da aka samu labarin rasuwarsa, iyalan marigayin na ci gaba da ƙoƙarin tara kuɗin fansar da masu garkuwar suka buƙata domin a sake shi.
“Har zuwa yanzu da aka samu labarin rasuwarsa muna ƙoƙarin haɗa kuɗin da ’yan bindigar suka nema domin a sako shi.
“Amma yanzu mun shiga cikin alhini matuƙa da labarin rasuwarsa a hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi,” in ji Aliyu.
Rasuwar Sheikh Muhammad Maibarga ta jefa iyalansa, almajiransa da al’ummar yankin cikin jimami, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya.