Sheikh Musa Muhammad: Tauraro mai haskakawa ya fadi

A yammacin ranar Asabar da ta gabata ce Allah Ya karvi rayuwar Babban Limamin Masallacin kasa da ke Abuja, Sheikh Musa Muhammad, bayan ya yi gajeriyar jinya a Babban Asibitin kasa da ke Abuja. Marigayi Sheikh Musa Muhammad wanda aka haife shi a garin Jos da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato […]

Sheikh Musa Muhammad: Tauraro mai haskakawa ya fadi
Sheikh Musa Muhammad: Tauraro mai haskakawa ya fadi

A yammacin ranar Asabar da ta gabata ce Allah Ya karvi rayuwar Babban Limamin Masallacin kasa da ke Abuja, Sheikh Musa Muhammad, bayan ya yi gajeriyar jinya a Babban Asibitin kasa da ke Abuja.

Marigayi Sheikh Musa Muhammad wanda aka haife shi a garin Jos da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato a ranar 11 ga Afrilun 1947 shekara 68 da suka gabata ya halarci makarantu daban-daban wajen neman ilimi, inda baya ga karatun allo da na azure ya kuma halarci Kwalejin Rimi College da Kaduna da kuma Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakwwato, kuma ya yi karatun nan na gidan rediyon Masar da ake kira Arabic by Radio duk a kokarinsa na zurfafa iliminsa da kuma tafiya da zamani.
Bayan gina Masallacin kasa a 1984, Marigayi Sheikh Musa Muhammad ya zama Na’ibin Babban Limamin Masallacin a 1991 wato shekara 24 da suka gabata, inda a shekarar 2009 Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar ya da shi a matsayin Babban Limamin Masallacin tare da nada masa na’ibai guda uku.
Kafin tabbatar masa da matsayin Babban Limamin an dan samu kananan maganganu inda wasu suka nemi sanya batun siyasar takardar ilimi suna cewa masu digiri ya kamata a nada, lamarin da ya jawo cece-ku-ce kafin Mai alfarma Sarkin Musulmi ya kawo karshen maganar ta hanyar tabbatar masa da limancin.
Wani babban jami’in a kwamitin Masallacin na kasa Ustaz Abubakar Siddiue ne ya fara tabbatar wa manema labarai da labarin rasuwar Sheikh Musa Muhammad inda ya ce za a yi masa jana’iza washegari Lahadi da karfe 10 na safe a Masallacin kasar.
Sheikh Musa Muhammad ya rasu ya bar mata hudu da ’ya’ya 14, kuma an bisne shi a makabartar Gudu da ke kusa da unguwar ’yan majalisa da ke Abuja. Kuma ya rasu ne bai fi saura wata biyu ba a fara gudanar da azumin Ramadan na bana ba, inda yake jagorantar Tafsiri ga sashin maza da kuma na mata baya ga hudubobi da laccocin da yake gabatarwa a mako-mako.
Dubban mutane ne suka halarci jana’izarsa cikinsu har da Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Mahmud Yayale Ahmed da Shugaban Hukumar Zave ta kasa Farfesa Attahiru Jega da Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar da Ministan Kimiyya Malam Abdu Bulama da tsohon Ministan Abuja Mohammed Abba Gana da zavavven Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Ganduje da tsohon Shugaban Jama’iyyar PDP ta kasa kuma Shugaban Kwamitin Yakin Zaven Shugaban Jonathan a zaven bana, Dokta Ahmadu Ali da kuma fitaccen malamin nan na Abuja Ustaz Abubakar Sadik da Sarkin Jiwa da sauran sarakunan Abuja da kuma manyan mutane da dama.
Daga cikin wadanda suka raka shi makwancinsa a makabartar Gudu, kuma daga cikin wadanda suka raka gawarsa har da zavavven Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da Ministan Abuja Sanata Bala Mohammed da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Alhaji Ibrahim Mantu da tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Adamu Aleiro da kuma Sanata Ali Ndume da sauransu.
Da yake ganawa da manema labarai kan rasuwar marigayin Alhaji Ibrahim Mantu ya bayyana cewa: “Lokacin da na samu labarin a jiya na kadu sosai, amma na san rayuwa tana hannun Allah ne, kuma Allah zai karve ta a duk lokacin da Ya ga dama.”
Shi kuwa Babban Limamin Masallacin Al-Habibiyya Imam Abdulganiu cewa ya yi marigayin mutum ne da ba ya da kabilanci wanda ya yi kokari sosai wajen hada kan al’ummar Musulmi. Sai ya yi addu’ar Allah Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa tare da ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.
Shi ma Babban Na’ibinsa Ustaz Ahmad Onilewura, ya roki Allah Ya gafarta wa marigayin tare da addu’ar Ya saka masa da Aljannar Firdausi.
A sakonsa na ta’aziyya zavavven Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayin a matsayin wani jigo na hadin kan al’umma. Janar Buhari ya ce rasuwar Sheikh Musa Muhammad wata komawa bay ace kan kokarin da ake yin a sake hade kan ’yan Najeriya bayan kamfe din rarraba kai da aka gudanar a lokacin da ake tunkarar zaven da ya gabata.
“Ya rasu a lokacin da ’yan Najeriya ke matukar bukatar shawarwarinsa don ci gaba da dinke kasa,” inji Buhari. Janar Buhari ya bayyana marigayi Imam Musa da jagora mai shiryarwa wanda yake wa’azin kaunar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a kuma wanda ya yi kokari a daukacin rayuwarsa wajen yaki da miyagun dabi’u da kuma rabbara kan jama’ar kasar nan.
“Ina yin ta’aziyya tare da sauran masu zaman makokinsa, kuma ina alfaharin tunawa da babban dan Najeriya. Allah Ya gafarta masa kuma Ya ba iyalansa da daukacin kasar nan hakurin jure wannan babban rashi,” inji Janar Buhari.
Babban Sakataren Jama’atu Nasril Islam ta kasa, Dokta Khalid Abubakr Aliyu da Shugaban Kwamitin Ganin Wata na Majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Malam Hafiz Wali, duk sun yi addu’ar neman gafara ga babban limamin tare da fatar Allah Ya saka masa da Aljannar Firdausi.
A sakonsa na ta’aziyya dauke da sanya hannun Bamikole Omishore, toshon Gwamnan Jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana limamin da fitaccen malamain addinin Musuluci, mai kyawawan dabi’u kuma wani babban tauraro na shiryar da al’ummar Najeriya.
Hakika Sheikh Musa Muhammad mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Musulunci hidima, kuma mutum ne mai sadaukar da kai wajen tabbatar da zaman lafiya da ’yan uwantaka a tsakanin al’umma. Tabbas al’ummar Najeriya musamman Musulmi sun rasa wani tauraro mai haskakawa da yake rungumar jama’a ba tare da nuna bambanci kungiya ko akida ko kabila ba.