Sheikh Pantami babana ne — Adaman Kamaye
Adama ta ce Minista Pantami kanin mahaifinta ne.
Zahra’u Saleh Pantami fitacciyar jaruma ce da aka fi sani da Adaman Kamaye a shirin ‘Dadin Kowa’ mai dogon zango da ake haskawa a gidan talabijin na Arewa24. A tattaunawarta da Aminiya, Adama ta bayyana alakarta da Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami da yadda ta shigo fim da dalilin da muryata take a shake da sauransu:
Ga tattaunawar Aminiya da ita:
Mene ne takaitaccen tarihinki?
Sunana Zahra’u Saleh Pantami, an haife ni a Jihar Gombe. Na yi karatun firamare da sakandare a Gombe. Duk wanda kika ji sunansa da Pantami a ciki, to dan gidanmu ne. Minista Sheikh Isah Ali Pantami kanin mahaifina ne.
- Mutanen da COVID-19 ta kashe a Gombe sun kai 60
- Japan ta kirkiro akwatin talabijin mai dauke da ‘dandanon abinci’
Daga baya na dawo wurin kakkanina da ke Garko a Jihar Kano. Ni ’yar kasuwa ce da ke kasuwancin atamfa da shadda da yadi da gidaje da motoci da sauransu. Na taba yin aure, ina da ’ya’ya uku.
Yaya aka yi kika shiga harkar fim?
Na shiga harkar fim ta hanyar aminiyata kuma uwar dakina, Hajiya Zulai Bebeji. Kasancewar na san ta tun a lokacin da muka yi zaman Saudiyya mun zauna a gida daya da ita. Da muka hadu da ita sai na gaya mata cewa ina son in shiga harkar fim.
Dama a ranar tana da wani aiki a wani fim na Musa Mai Sana’a a Kabo Guest Inn, don haka sai ta nemi mu je tare. Da muka je sai ta gaya wa Mai Sana’a cewa ni ’yar uwarta ce ina son shiga fim. Don haka sai ta nemi ya ba ni matsayin da za ta fito a cikin fim din. Amma sai shi Mai Sana’a ya ce ba sai an yi haka ba, don akwai wani wuri da zai iya sanya ni.
A takaice dai a nan ya sa ni a fim dinsa wanda ya zama shi ne fim dina na farko wato fim din Akwai Hisabi, daga nan kofa ta bude. Kuma abin da ya sa na shiga fim saboda na ga fim sana’a ce. Kuma abu ne na nishadi da ilimintarwa. Haka Sani SK da marigayi Ahmad Tage da Alasan Kwalle su ne suka tsaya min a matsayin garanto.
Lokacin da aka kira ni audition na Dadin Kowa a Arewa 24, mun fi mu 70 da muka nemi fitowa a matsayin Adama, amma ni Allah Ya ba nasara. Dukkanmu mun shiga gwaji aka gaya mana abin da za mu fadi muka je muka gwada aka dauke mu a kyamara sannan aka tantance aka zabe ni.
An yi kwanaki da yin gwajin sai daya daga cikin daraktocin fim din da ake kira Adamu ya kira ni a waya ya ce ni aka zaba zan fito a matsayin Adama don haka ana nemana a Arewa don fara daukar aikin.
Na yi murna sosai da jin haka, kasancewar ina matukar son aikin.
Shin akwai wata alaka a tsakaninki da Kamaye?
Gaskiya alakar da take tsakaninmu alaka ce ta mutunta juna domin yana daukata a matsayin ’ya ni kuma ina daukarsa a matsayin uba. Idan ya ga na yi kuskure yakan yi min fada irin na uba da ’ya domin in gyara amma babu wata alakar soyayya a tsakaninmu.
A yanzu haka idan da zan kawo wa Kamaye mutumin da nake so da aure, to insha Allahu zai wuce gaba wajen gabatar da komai na auren.
Kina shirin yin aure nan kusa ke nan?
Yanzu ba ni da aure amma a shirye nake in yi aure idan Allah Ya ba ni abokin rayuwa wanda ya cancanta da abin da nake bukata. Amma duk da haka mutum sai ya bi a hankali kasancewar yanzu duniya mutane babu amana. Kuma kin san an ce idan wuta ta kona ka ko toka ka ga ni sai ka gudu.
Akwai jita-jitar cewa shakewar muryar da kike da ita tana da alaka da shaye-shaye, mene ne gaskiyar lamarin?
Ba yanzu na fara jin wannan magana ba, amma gaskiya ba haka ba ne. Ba na shan komai sai ruwa, abin da ya faru na samu matsala ce a makogwarona hakan ya shafi muryata. Sau uku ana yi min aiki a makwagwaron amma ba a yi nasara ba.
Wata rana Hajara Usman ta shawarce ni in je wajen wani asibitin kunne da hanci da makogwaro. Kasancewar ta taba yin wani hadari da ta samu matsala a kunne. Da na je asibitin likitan ya yi min aiki. To haka dai na yi ta fama sau uku ana yi min aiki.
Yanzu ma alhamdulilah na samu sauki a kan baya idan na yi magana ana ji.
Kwanan nan wasu hotunanki tare da wani saurayi sun rika yawo a shafukan sada zumunta, har wadansu na cewa Adama ta yi wuf da wani yaro, mene ne gaskiyar wadannan hotuna?
Su dai wadanann hotuna ba na gaskiya ba ne, babu wanda na yi wuf da shi. Hotuna ne da muka dauka don sanya wa a fosta din wani sabon fim dina mai suna ‘Matar Yaro’. Wannan ne fim din da na dauki nauyi da kudina, kuma ni ce jarumar fim din, sabanin sauran fina-finan da nake fitowa a matsayin jaruma kawai.
Fim din Matar Yaro yana dauke da darussa da dama, yana kuma ilimintarwa a kan a daina kyamar matan da suke auren mazan da suka girma. Duk da cewa ba haram ba ne a addini amma za ki ga cewa duk yayin da mace ta yunkuro za ta yi aure da wanda ta girma, sai ki ga an dauki magana ana zagin ta da saurasnu. Mun san cewa kafin wani ya yi wannan abu Manzon Allah (SAW) ya yi.
Wane sako kike da shi ga dimbin masoyanki?
Ina mika godiya gare su, sannan ina kira gare su cewa ni mutum ce mai karbar gyara. Duk inda aka ga na yi kuskure to don Allah a ja hankalina a kai. Wannan ne soyayya ta gaskiya. Ni a rayuwata ina girmama mutum domin arzikina na mutum ne. Da mutane nake cin arziki a duniya. Ita kanta duniyar arzikin Manzon Allah (SAW) take ci.
Haka ina kira ga masoyana su rika yi mana uzuri domin akwai wadanda za su kira mutum to, watakila a samu kiran bai shiga ba ko ya shiga amma saboda wasu uzurirrika ya kasance ba ka amsa ba. Amma sai mutane su je suna yi maka wata fassara ta daban, wai kai mai wulakanci ne da sauransu.
Haka za ki ga wadansu mutanne suna nemanmu ta shafukan sada zumunta amma saboda sun yi yawa sai ki ga mutum bai samu damar amsa wa wadansu ba. An dai ce idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai, abin sai a hankali a rika yi mana uzuri.