Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya rasu
Ana sa ran gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe biyu 2:00 na rana a Masallacin Santa, Unguwar Rimi cikin birnin Jos.

Allah Ya yi wa babban malamin Musulunci a Najeriya Sheikh Sa’idu Hassan Jingir rasuwa, bayan fama da rashin lafiya.
Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na Ƙasa na Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS).
Ana sa rana gudanar jana’izarsa da misalin ƙarfe biyu 2:00 na rana a Masallacin Santa, Unguwar Rimi cikin birnin Jos.