Sheikh Yasser Dossary ya dawo limanci a Masallacin Harami

Sheikh Sudais ya sanar da dawowar Sheikh Yasir Ad Dawsary limanci a Masallacin Harami da wasu limamai biyu a Masallacin Madina

Sheikh Yasser Dossary ya dawo limanci a Masallacin Harami

Yasser Dossary

Babban Limamin Masallatan Harami Sheikh Abdul Rahman al-Sudais, ya sanar da dawowar Sheikh Yasser Dossary da wasu limamai biyu.

Sheikh Sudai ya sanar cewa Sheikh Yasir zai ci gaba da limanci a Masallacin Harami da ke Makkah.

Sauran limamn biyu, Sheikh Khalid Muhanna da kuma Sheikh Ahmad Hudhaify, za su ci gaba da limanci ne a Masallacin Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi Wa Sallama da ke Madina.

Sheikh Sudai, ya roki Allah “Ya yi musu jagora Ya ba su dacewa a cikin limancinsu ga al’ummar Musulmi,” in ji sanarwar da Hukumar Gudanarwar Masallatai Masu Alfarma ta fitar.

Wannan albishir daga Sheikh Sudais ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin fara azumin watan Ramadan na bana.

A baya dai ana fargabar malaman ba za su yi limanci ba a watan Ramadan, saboda karewar wa’adin kwantiraginsu na shekara huɗu a masallacin.

Da haka adadin limaman masallacin Harami zai sake komawa 8 kamar haka:

1- Sheikh Abdur Rahman As Sudais

2- Sheikh Abdullah Awad Al Juhany

3 – Sheikh Maher Al Muaiqly

4- Sheikh Bandar Baleelah

5- Sheikh Faisal Ghazzawi

6- Sheikh Saleh Al Humaid

7- Sheikh Usaamah Khayyat

8- Sheikh Yasser Dossary

Shekarar 2015 Sheikh Dawsary ya fara limancin sallar Taraweeh a Masallacin Harami a matsayin bakon liman, kafin shekarar 2019 Masarautar Saudiyya ta nada shi a matsayin cikakken limami, wanda za a rika sabunta kwangilarsa bayan shekara hudu.