Sheikh Yusuf Sambo ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kammala aikin jawo ruwa daga teku zuwa Arewa

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Yusuf Sambo Rigachikun ya bukaci Gwamnatin Tarayyar ta kammala aikinjawo ruwa daga teku zuwa garin Lakwaja da ke nan Arew da gwamnatin marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ta faro. Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum ya bayyana haka ne a lokacin […]

Sheikh Yusuf Sambo ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kammala aikin jawo ruwa daga teku zuwa Arewa

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Yusuf Sambo Rigachikun ya bukaci Gwamnatin Tarayyar ta kammala aikin
jawo ruwa daga teku zuwa garin Lakwaja da ke nan Arew da gwamnatin marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ta faro.
Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi a wurin wa’azin kasa da kungiyar ta shirya a garin Lakwaja, inda ya ce babu kammala aikin yana da matukar muhimmanci, domin zai ba jiragen ruwa zuwa Arewa suna kawo kayayyaki inda yin hakan zai kawo ci gaba a Arewa da Najeriya baki daya.
Shaihin Malamin ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta hanzarta kammala aikin hanyar Lakwaja zuwa Abuja, domin a samu raguwar yawan haduran da ake samu a hanyar.
Sheikh Rigachikum ya ce, “Mu ’yan Arewa muna alfahari da garin Lakwaja domin nan ne hedkwatar Najeriya ta farko kafin a koma Legas.
A nasihar Shugaban Majalisar Malaman, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce akwai bukatar gyara a Najeriya kan halin da muke ciki.
Ya ce “Allah Ya yi mana arziki, don haka bai kamata mu shiga halin kuncin da muke ciki ba. Hanyar fita daga cikin wannan hali ita ce mu hada kai a kan gaskiya kowa ya tsaya ya yi aikinsa tsakani da Allah, kuma mu gyara kuri’unmu mu zabi shugabanni nagari.”
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Idris Wada kan kokarin da gwamnatin jihar ta yi wajen daukar nauyin gudanar da wa’azin. Ya ce  a kokarin da kungiyar take yi na yada ilimi a kasar nan, sun
gina makarantar makiyaya a Imewuro da ke jihar. Kuma ya roki Gwamnan ya tallafa wa makarantar ta makiyaya da suka gina.
A nasa jawabin Gwamna Idris Wada ya yi kira ga Musulmin Najeriya ne kan su hada kansu. Ya ce addinin Musulunci addini ne da yake koyar da hadin kai da zaman lafiya da kaunar juna.