Shekara ɗaya da harin Tudun Biri har yanzu da sauran rina a kaba

Al’ummar ƙauyen Tudun Biri inda jirgin soji ya kai harin bom kan masu taron Maulidi sun ce shekara ɗaya bayan harin har yanzu ba a fara maganar biyan su diyya kamar yadda aka yi alƙawari ba

Shekara ɗaya da harin Tudun Biri har yanzu da sauran rina a kaba

A yayin da ake cika shekara guda bayan  harin bom da jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya ya kai wa masu taron bikin Maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, al’ummar yankin sun ce har yanzu ba a fara biyan su diyyar da aka yi alƙawari ba kan waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata.

Zuwa yanzu iyalan waɗanda abin ya shafa a Tudun Biri sun ce ba a kammala cika masu alƙawuran da aka ɗauka musu ba, mahukunta su fi mayar da hankali wajen gine-gine a garin.

Sun kuma bayyana damuwa cewa mahukunta sun yi watsi da makwabtansu irin su kauyen  Ugara da su ma suka rasa mutane a harin da ya auku a Tudun Biri.

Mutane sama da ɗari ne suka halaka a harin Tudun Biri, cikinsu har da maza da mata da ƙananan yara da suka halarci taron bikin Maulidi daga ƙauyen da maƙwabtansu. Adadin mutanen da suka samu raunuka kuwa ya zarce waɗanda suka halaka.

Lamarin ya auku ne a ranar 3 ga watan Disambar shekarar 2022 da misalin ƙarfe 10 zuwa 11 na dare, a yayin da jirage marasa matuƙa wintairi

Bayan kai waɗannan hare-hare waɗanda suka matukar tayar da hankulan al’umma a ciki da wajen Najeriya, ya sa gwamnati da ’yan majalisu musamman na ƙasa suka yi tururuwa zuwa Jihar Kaduna domin jajanta wa gwamnatin jihar tare da bayar da tallafin kuɗaɗe domin kulawa da waɗanda iftila’in ta shafa.

Sai dai da tun bayan wannan hari, har ya zuwa yanzu iyalan waɗanda abin ya shafa sun ce ba a kammala cika masu alƙawuran da aka ɗauka ba, an fi mayar da hankali wajen gine-gine a garin.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka rasa yayansu mai suna Bello, ya shaida wa Aminiya cewa ana dai ƙoƙarin cika alƙawuran gyaran garin na Tudun Biri kamar yadda gwamnatin ta yi alkawarin yi.

“Yau kusan shekara ɗaya ke nan da aukuwar wannan lamari inda na rasa ’yata da kuma wasu ’yan uwa da suka raunata.
“Kuma an dai ba mu wasu ’yan kuɗaɗe daga cikin waɗanda aka ce an tara da sunan taimaka mana,“ in ji shi.

Ya ƙara da cewa batun gidaje da aka ce za a gina a Tudun Biri tuni an fara, kuma an kammala aikin asibiti da ginin wajen koyar da sana’oi sannan ga aikin hanyar garin da ake kan yi.

Sai dai Bello ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna da su duba sauran kauyuka irinsu Ugara da su ma suka rasa mutane a harin da ya auku a Tudun Biri, ta wajen Gina musu hanyar mota kamar yadda aka yi wa Tudun Biri da samar musu da asibiti da makaranta saboda a cewarsa, su ma ’yan Ugara sun rasa mutane a harin na ranar 3 ga watan Disambar bara.

Shi ma ɗaya daga cikin mazauna yankin mai suna Liman, ya tabbatar da ci gaba da aikin hanya da asibiti da wajen koyan sana’o’i da gidaje.

Amma ya buƙaci a waiwayi mutanen da suka rasa ’ya’yansu da ’yan uwansu wajen biyan su diyya.

“Gwamnati tana ƙoƙari wajen cika alƙawarin samar da gidaje da asibiti da hanyar garin, sai dai babu labarin ko za a bai wa mutane diyya, domin abin da aka biya mutane suna ganin daga cikin taimakon da aka bai wa gwamnatin jihar ne, a madadin waɗanda iftila’in ya shafa, amma ba da sunan biyan diyya aka biya ba,” in ji shi.

Liman ya bayyana cewa kwanan nan ne aka kammala aikin asibiti na farko a garin, wanda kuma ake sa ran Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, zai buɗe a ranar Lahadi a garin na Tudun Biri.

“Aiki kam na ci gaba domin gwamna ne ake sa ran zai zo ya buɗe asibitin da aka kammala ginawa domin amfanin jama’ar yankin.

“Sai dai muna rokon da a cika dukkan alƙawuran da aka yi wa mutanen yankin,” in ji shi

A watannin bayan Aminiya ta ziyarci garin inda ta kawo rahoton yadda aka ƙaddamar da fara aiki da masallacin da ake ginawa garin a karon farko tun bayan harin bom ɗin.

Pix1: Hoton inda aka bizne wayanda suka rasu a ranar 3 ga Watan Disambar 2023.

Pix 2: Masallacin Juma’a da wani bawan Allah ya Gina a garin