Shekara 1 da hatsarin jirgin Janar Ibrahim Attahiru

Babu wanda ya tsira a hatsarin jirgin Janar Attahiru tare da ’yan tawagarsa, manya da kananan sojoji

Shekara 1 da hatsarin jirgin Janar Ibrahim Attahiru

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

A ranar 21 ga watan Mayu, 2021, Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru ya rasu a wani hatsarin jirgin saman soji a Kaduna.

Janar Attahiru ya rasu ne tare da daukacin ’yan tawagarsa a lokacin da suka kan hanyarsu ta zuwa halartar taron yaye kuratan sojoji a Zariya.

Ajajlin nasu, wanda ya girgiza Najeriya da ma sassan duniya, ya dauke su ne a sakamakon rashin kyawun yanayi.

Lamarin ya sa jirgin ya yi hatsari, kuma babu mahalukin da ya tsira a hatsarin da ya auku lokacin da jirgin ke kokarin sauka a Filin Jirgi na Kasa da Kasa da ke Kaduna.

Janar Attahiru mai shekara 54 ya rasu ne ba jimawa da zamansa Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya bayan magabacinsa, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai.

Gabanin rasuwarsa, ya bayyana aniyarsa ta ganin sojoji sun murkushe kungiyar Boo Haram, wadda aka shafe sama da shekara 12 tana addabar Najeriya.

A farko-farkon jagorancinsa, Janar Attahiru ya rika ziyartar sojoji a filin yaki yana ganawa da su tare da ba su kwarin gwiwa da kuma tabbacin samun abubuwan da suke bukata domin cim ma nasara a yaki da ta’addanci.

A ranar Lahadi, 23 ga watan Mayu 2021, aka yi musu jana’izar soja a makabartar sojoji da ke Abuja, cikin yanayi na kaduwa da jimami.

Hatsarin jirgin Janar Attahiru da hafsoshi 10 gami da kananan sojoji da ke ciki, ya auke ne wata uku bayan wani hatsarin jirgin soja da ya kashe mutum bakwai da ke cikinsa a Abuja.

Hatsarin jiragen soji sun yawaita a baya-bayan nan a Najeriya, na baya-bayan nan shi ne wanda ya yi ajalin matukansa biyu a Kaduna.

Kafin shi wani jirgin yaki ya rikito a yayin da yake tsaka da yaki da ’yan ta’adda a yankin Jihar Zamafa; amma an yi sa’a matukinsa ya yi saukar lema.