Shekara 100 da haihuwar Najeriya
Idan muka waiwaya baya tun lokacin da Turawan mulkin mallaka suka mamaye yankin Kudu da kuma Arewacin, inda ake kira Najeriya a yau, wadda aka rada wa suna a 1914. Za mu ga irin kangin bauta da akuba gami da rashin ‘yancin walwala wanda sarakuna, malamai, iyayenmu da kuma kakkaninmu suka dandana a hannun Turawa.Bayan […]
Idan muka waiwaya baya tun lokacin da Turawan mulkin mallaka suka mamaye yankin Kudu da kuma Arewacin, inda ake kira Najeriya a yau, wadda aka rada wa suna a 1914. Za mu ga irin kangin bauta da akuba gami da rashin ‘yancin walwala wanda sarakuna, malamai, iyayenmu da kuma kakkaninmu suka dandana a hannun Turawa.
Bayan tafiya ta yi tafiya suka fahimci cewa idan al’amura suka ci gaba da tafiya a haka to hatta ‘ya’ya da jikokin da zasu haifa nan gaba, suma za su kasance a cikin kangin bauta. Daga nan tashi fadi da kuma gwagwrmaya wadda ta kunshi sadaukarwa da kai da kuma dukiya, dole tasa Turawa suka kawo karshen mulkin mallaka suka bada ‘yancin kai. Allah ya saka wa iyaye da kakanninmu da alheri sakamakon sadaukarwa da suka yi, wasu sun yi watsi da jin dadinsu, sun bar alfarmar gidajen sarauta da gatar iyaye don ganin wadanda za su zo bayansu sun samu rayuwa mai ‘yanci gami da walwala.
Hakan ya tabbatar da samun ‘yancin kai a 1960, wanda ya samu sakamakon ‘yan siyasa masu kishin kasa, masu kishin al’ummarsu, wanda kasar ce gabansu ba aljihunsu ba, bayan sun mutu ba abin da suka bari, ba su nuna bambamcin addini ko kablianci, suna da kudurori da manufofi masu kyau, inda suka gina kasa bisa kyakyawar turba. Mafi yawan ‘yan kasa sun gamsu da salon mulkinsu, kowa na ganin kasar za ta kai tundun tsira.
Kwatsam rana tsaka aka samu wasu marasa tsoron Allah, maras tausayi ko kishin kasa, suka wa wannan jaririyar ta’addanci, suka jefa ta cikin kangin rayuwa da tarin matsaloli, wanda har yanzu an kasa magancesu, ta hanyar kashe jagorori masu kishin kasar da al’ummarta. Najeriya ta kasance cikin maraici na rashin uwa, a lokacin tana cikin tsumman goyo. Ta fada hannun mulkin soji karo na farko a 1966, mulklin da ya assasa kabilanci da kuma bangaranci a gwamnati, har aka hambare su. Jaririyar kasar ta kara komwa hannun wani sabon shugaban mulkin soja, sai ga wata sabuwar annobar Yakin Basasa, wadda aka shekaru uku ana gwabzawa.
A Jamhuriya ta biyu a 1979, an cika da burin samun ci gaban kasa da wadatuwar arziki, yayin da aka yi watanda kowa ya yi gaban kansa, ake neman barin kasa a makance ba jagora, sai sojoji suka kasa kutso kai wadanda suka yi kakagida har zuwa 1999.
Najeriya ta koma kan tafarkin dimokuradiyya, aka yi bikin cikin murna da fatan samun ingantacciyar rayuwa. Gwamnatin farar hula ta ‘yan siyasa ta yi alkawarin samar da ababen more rayuwa, da suka hada da samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma da ingantaccen tsarin kiwon lafiya da ilimi wadataccen ruwan sha da aikin gona da dai sauran ababen da suka shafi rayuwar jama’a.
Abin takaici, a yau Najeriya da ta cika shekaru 100 da dunkulewa, shekaru 53 na ‘yancin kai, shekaru 14 na dimokuradiyya. Gwamnatin farar hula ta gaza cika wa jama’a alkawurran da ta yi musu. A kullum alkawarin da ake yi shekaranjiya da jiya shi ne ake maimaitawa a yau da kuma gobe. kasar ta fita daga hayyacinta. Babu ta yi yawa, a kullum asarar rayuka ake yi. Ba mai tabbas a game da rayuwarsa.
Asibitocinmu ba kwararrun liktoci ba magani! Yajin aiki da rashin kayan aiki ya mayar da harakar ilimi baya. Rashin wutar lantarki ta durkusar da masana’antunmu, sun zama gwangwani. Harkar sufuri musamman jiragen sama da na kasa ya zama tarihi. Titunanmu sun zama tarkunanmutuwa.
Ruwan sha sai dai rijiya ko rafi, maganar ruwan fanfo ya wucemu! Harkar nona da kiwo gara jiya da yau, uwa uba cin hanci da rashawa abin da ya mamaye kusan duk harkokin gwamnati da kasuwancin kasar, kowa na cutar kowa, har yana neman kai mu ga kushewa.
Lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su hada kai, ba tare da nuna bambancin addini ko na siyasa ko kuma na kabilanci ba, mu yi aiki tare bisa gaskiya da rikon amana, domin kawar da mulkin zalunci da azzalumai.
Zan mana wata matashiya a nan, idan muna rera taken kasarmu muna yi wani baiti kamar haka “Wahalar da jarumanmu suka sha ba za ta tafi a banza ba”.
Tarihi baya mantuwa balle yafiya. Kuma dukkan abin da mutum ya shuka shi zai girbe. Ya zama wajibi akanmu mu sauke nauyin dake kanmu ta hanyar tsallakar da kasar nan zuwa tundun mun tsira. Domin ‘ya’yanmu da jikokinmu da zasu zo nan gaba su sami rayuwa mai inganci. A nan ina addu’a ga shugabanni na kwarai, masu kishin kasa da al’ummarta, Allah saka masu da alherinsa ya kuma gafarta masu kurakuransu. Ya arzutamu da jagorori masu son ci gaban kasa marar kutungula, Ya Allah kada ka ba su nasara, Ka yi mana jagora zuwa ga tafarki madaidaici. A karshe ina wa wannan kasa fatan tsawancin kwana, Allah ja kwanan mahadi, amin
Jibril Abdul Daura 08038997861 Tudun Wada, Daura-jihar Katsina