Shekara 100: Kaduna ga tsufa ga kuruciya
Turka-turkar takun tsalle-tsallen kofaton doki da rakumi da ya gudana a Kaduna wajen hawan Dabar bikin cikar birnin shekara 100 ya tunatar da ni kan samar wa birnin katin tunawa da ranar kafuwarsa, tunda nan ne ya kasance gidana na biyu. A yau Kaduna cike take da matasa wadanda suka fi sanin shafukan intanet fiye […]

Turka-turkar takun tsalle-tsallen kofaton doki da rakumi da ya gudana a Kaduna wajen hawan Dabar bikin cikar birnin shekara 100 ya tunatar da ni kan samar wa birnin katin tunawa da ranar kafuwarsa, tunda nan ne ya kasance gidana na biyu. A yau Kaduna cike take da matasa wadanda suka fi sanin shafukan intanet fiye da dawakai. Domin hamshakin hawan Dabar da aka yi na karshe shi ne na shekarar 1977 a matsayin wani yanki na bikin al’adun FESTAC. An gudanar da hawan Daba da dama cikin shekarun 1950 har zuwa shekarun 1970 a matsayin bukukuwan tarihi, amma ta yiwu mafi kimar girman Daba da ba a yi kamarta a Kaduna ba ita ce ta 1956, lokacin ziyarar Sarauniyar Ingila Elizabeth II a Najeriya, a lokacin da ta hau karagar mulkin Birtaniya da shekara uku.
Wurin da aka gudanar da hawan Dabar shi ne dandalin Murtala, wanda a da ake kira da filin sukuwa, wanda a halin yanzu ya zama kufai.An mamaye mafi yawan fadin wurin da wuraren shakatarwa, ‘kulob-kulob,’ da shaguna da bankuna da wuraren motsa jiki da hukumar wasanni, tare da runfunan da aka gina lokacin da Kaduna ta dauki nauyin gudanar da bikin al’adu na FESTAC shekaru da dama da suka wuce, da kuma dakin taro na Umaru ’Yar’aduwa. Ina dai cike da mamakin ganin cewa har yanzu akwai isasshen wurin hawan Daba.
Shin shekarun Kaduna da kafuwa 100 ne ko kuma ta zarta hakan? Akwai wani rudani game da shekarun. Domin a shekarar 1917 ita ce shekarar da Gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya ta mayar da Kaduna babban birnin Arewacin Najeriya, bayan sun taso daga Zungeru, wadda take cikin Jihar Neja ta yanzu, inda daga bisani aka matsa zuwa Lokoja. Sai dai kamar yadda Dokta Yusuf Nadabo ya yi nuni a mashahurin littafinsa mai taken: Tarihin Garin Kaduna (wanda na fara karantawa a shekarar 1988), kafin Lugard ya koma can, kauyuka ne kawai a tattare da kewayen birrnin Kaduna ta yau, wadanda suka hada da Kinkinau da Kawo da Mando da sauran kauyukan Gwari (Gbayi) da ke Kakuri da Makera. Sannan akwai wani babban wuri da ake kira Unguwar leburori (wato sansanin leburrori), inda leburorin da suka gina titin jirgin kasa da ya hade tsakanin Kudu da Arewa aka yi musu masauki.. wannan wurin shi ne a yau ya zama Tudun Wada.Kuma mashahuriyar gadar jirgin kasar nan da ta tsallaka kogin Kadun an yi ta ne a shekarar 1911.
Lokacin da aka kaddamar da littafin Nadabo a shekarun 1980 sai al’umma Gbayi (Gwari) suka yi zanga-zanga kan cewa Hausawa na so su kwace garin Kaduna daga Gbayi, kamar yadda tarihi ya tabbatar. Wannan labari ya yi matukar amfani lokacin da nake Editan jaridar New Nigerian a Kaduna a shekarar 2015. Yaron da ke hidima a ofishina mai suna Bulus, wanda shi ma dan kabilar Gbayi ne, ya shigo ofishina tare da nuna jin kunya a wani yammacin ranar juma’a, inda yake ta shafa kansa, sai ya ce, “Oga ba mu gane kan wannan garin ba fa!” yana kokarin nuna mini cewa ba shi da kudin kashewa a karshen mako. Da na tuna rikicin da ake yi kan ko wane ne ya mallaki garin Kaduna, sai na ce, “Bulus, ku kuka ce kune masu garin nan. Idan har ba ku gane ba, ta yaya kake zaton sabon zama irina zai san gaba ko bayansa!”
Tun lokacin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce Kaduna ta cika shekara 100 da kafuwa, sai nake ta kokarin tattara al’amuran tarihi da suka faru a gabana a wannan birni. Tun ina yaro dan shekara uku nake zaune a Kaduna cikin shekarun 1960, kuma na sake zama na tsawon shekara 17, wato daga 1990 zuwa 2007. Don haka na zauna a Kaduna tsawon kimanin kashi daya bisa biyar (1/5) na wadannan shekaru 100. Akwai tsofaffin zama a Kawo da Tudun Wada da Unguwar Sarki da Kakuri da Barnawa, wadanda suka kasance a Kaduna tsawon wadannnan shekaru 100, don haka nake kiran kan a yi aikin tattara labarinsu kafin su mutu.
Kaduna na da dimbin tariohi, koda a ce ba a yi wani katabus ba wajen tattara su. Akwai dakin taro na Lugard Hall, wato mazaunin tsohuwar majalisar dokokin Arewa. Akwai Unguwar Shanu, inda Nadabo ya ce Lord Lugard yake tara garken shanu. Akwai Kabala Doki, inda ’yan sanda suka rika tara dawakai. Akwai Kabala kashi (yanzu ana kiranta da Kabala West), inda aka rika zubar da kashin da aka yashe daga masai. A wadannan kwanakin na cika da mamakin yadda Badarawa ta bunkasa ta zama mai kayatarwa, domin mahaifina ya fada mini cewa lokacin da ya samu halartar Kwalejin Kaduna a shekarar 1944 babu ita. Ya ma tuna cewa mutumin farko da ya fara zama a wajen, tsohon sojan da ya yi yakin duniya na biyu ne, wato Mamman Badarawa.
Kaduna ta kasance matattarar sojoji tun zamanin mulkin mallaka. Titin WAFF Road, an yi masa lakabin ne don rundunar sojojin Afirka ta Yamma, wato West African Frontier Forces na zamanin mulkin mallaka, wanda daga bisani aka sake masa suna zuwa titin Muhamamdu Buhari a shekarun 1990. Makarantar horar kananan hafsoshin sojojin Najeriya ta NDA da runduna ta daya da ke barrikin Dalet, barikin sojan kasa na atilare da ke Kalapanzi da ke Kakuri da sauran gidaje da wuraren horar da sojoji, ga asibitin soja na 44 tare da Kwalejin Command and Staff da cibiyar sojan kasa da makarantarsu da ke Jaji, sannan ga manyan rukunin gidaje a Kaduna.
Dadin dadawa Cibiyar horar da ’yan sanda da barikin ’yan sanda, tare da sauran wuraren aiki. Ta yiwu sakamakon hakan, akwai daruruwan janar-janar din soja da suka yi ritaya da ke zaune a Kaduna, kuma an san da zamansu. A shekarar 1994 lokacin da marigayi Dokta Shehu Lawal yake babban sakataren Kantoman mulkin soja ya gaya mini cewa gidan gwamnati yana da matakan da ake bibiya har 100 na Janar-janar da suka yi ritaya da ke zaune a Kaduna. Ya ce lokacin da Kanar Lawal Jafaru Isa ya kama ragama a matsayin Gwmanan Soja, Shehu ya raka shi ya ziyarci kowane daya daga cikinsu.
Tsohuwar Gwmnatin Arewa da aka shafe ayyukanta shekaru 50 da . cibiyoyin da ke karkashinta sun hada da Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Kaduna da Hukumar kula da kadarorin Arewa (ICSA) da aka rushe a shekarar 1975, amma har yanzu ana jin tasirinta a Kaduna. Manyan cibiyoyin da ke karkashinta sun hada da Kwalejin kimiyya da fasaha ta kaduna da kamfanin raya Arewa na NNDC da kamfanin kafa masana’antun Arewa da rukunin otal-otal din Arewa da otal din Hamdala da filin wasa na Ahmadu Bello da Sakatariya da gidan talabijin na Kaduna (yanzu gidan Rediyon Najeriyta na Kaduna FRCN da gidan talabijin na Najeriya NTA) da Asibitin Koyarwa (yanzu Jami’ar Jihar Kaduna) da asibitin Nursing Home (yanzu Asibitin Barau Dikko) da Gidan gwamnati (yanzu gidan Hassan Usman Katsina), su ne muhimman wuraren da suka bayyana Kaduna karara. ICSA ta raba gidajen ministoci, wadanda suka zama ofisoshin gudanar da harkokin jihohi. Wasu daga cikin hukumomin yankin Gwamnatin tarayya ta karbe su. Baya ga haka, Kaduna na da dimbin cibiyoyin gwamnatin tarayya, wadanda suka hada da wajen adana kayan tarihi na kasa da dakin karatu na kasa da cibiysar nazarin cutar kudan tsando, da cibiyar jami’an hulda da jama’a ta kasa NIPR da Sakatariyar Gwmanatin Tarayya da Kwalejhin Gwmnatin Tarayya da cibiyar horar da malamai (NTI) da cibiyar kula da kwalejojin fasahar kere-kere ta kasa (NBTE) da Hukumar ilimin makiyaya ta kasa.
Muhimmin mutumin da ya fi kowa kimar mutuntaka a tarihin Kaduna shi ne Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Tambarin mulkinsa na tsawon shekara 12 har yanzu ana ganinsa a tsohon gidansa na Arewa House da tsohon ofishinsa da ke gidan Hassan Usman Katsina, da tsohon wajen wasan kwallon fibes dinsa, wanda ke gefen gidansa na Arewa House kan titin Rabah da Marnoma da degel da Sultan Bello da tittin Sultan. dimbin mazauna Kaduna na wannan zamanin ba su san cewa wadannan titunan sunayen garuruwan Sakkwato ne ba, haka suke furta sunayensu cikin barkwanci.
daya daga cikin munanan al’amuran da suka faru a tarihin Kaduna a baya-bayan nan, gwargwadon sanina, shi ne kufan masana’antu da ke wannan birni a Kakuri da Makera da Kudenda, al’amarin da ya haifar da rushewar masaku tsawon shekara 40, wadanda suka kasance su ne mafi kima wajen bayar da ayyukan yi. kari a kan haka shi ne rushewar hada-hadar jirgin kasa (wadda a da ba a tantamar zuwansa a mahadar Kaduna); kassara kamfanin motoci na Fijo da matatar Kaduna; da durkushewar Kamfanin bunkasa Arewa da kamfanin kafa masana’antu na Arewacin Najeriya NNIL da otal-otal din Arewa da jaridar New Nigerian; ba ma tare da an ambaci lalata otal din Durbur da aka yi ba. Wuraren masana’antu, wadanda ada ake hada-hadar jama’a babu kakkautawa yanzu sun zama kufai tamfar makabarta saboda illar fasakwauri da hada-hadar kasuwancin duniya da faduwar darajar Naira da rashin makamashin wutar lantarki.
A wajen taron ‘’yan jarida da aka gudanar kan yadda za a gudanar da bikin cika shekara 100 na Jihar Kaduna, Sakataren Gwamnatin Jiha Balarabe Lawal ya nuna takaicinsa kan yadda aka raba kan al’ummar jihar bisa la’akari da addinansu. Gwmana Nasir el-Rufa’i shi ma ya yi bayani kan hakan, inda ya bayyana a jawabinsa cewa dimbin abubuwan ban takaici sun faru a tarihibn baya-bayan nan na Jihar Kaduna. Ni ma a kashin kainan na tabbatar da aukuwar al’amura hudu na rikice-rikicen kabilanci da addini lokacin da nake zaune a Kaduna, yayin da biyu suka auku a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2012, lokutan da na rika kai ziyara. Sakamakon wadannan rikice-rikicen , birnin ya rabu tsakanin mabiya addinai, wato musulmi a Arewa, Kirista a Kudu.
Dangane da zamantakewar rayuwa a Kaduna., ina kwarin gwiwar tabbatar da cewa gari ne na ’yanci. Lokacin da na koma Kaduna ina gwauro a shekarar 1990, bayan na fito daga yankin masu ra’ayin rikau na Sakkwato, na samu rayuwa mai armashi a Kaduna saboda hadakar mabambantan mutane, inda kowa ke da ‘’yancin walwala ‘shaidan kawai ke da dmauwa. Ba gaskiya ba ne cewa na yi matukar damfaruwa da son Kaduna.