Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 1

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka: An samu nasarar dimkoradiyya – Sabo Musa […]

Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 1
Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 1

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

An samu nasarar dimkoradiyya – Sabo Musa Katsina

Malam Sabo Musa, Matasa Motors Katsina: “Ni dai da ke Katsina shekara 14, mu kam sai son barka; gaba muka ci sosai saboda duk abin da muke so na ci gaba, mun samu akalla kashi 85 cikin 100 na ci gaba. Wajen ilimi, an yi mana makarantun firamare sama da 200, an yi mana makarantun sakandare sama da 150; ga makarantun koyon sana’a da asibitoci sama da100 da sabbin asibitoci. Haka kuma an gina hanyoyi sama da 50, ga filin jirgi, ga masallatai sama da 300 da makarantun islamiyya sama da 300. An gyara mazaunin Hukumar Alhazai na Katsina.
“A fannin noma, an sayo motocin noma, an gina gidaje a Katsina da kewaye, ana tura yara karatu kasashen waje, musamman ’ya’yan talakawa. Ana biyan ma’aikata sabon tsarin albashi, ana daukar sabbin malaman makaranta ba adadi.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50