Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 2

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka: Ba a samu nasara ba – Muhammad […]

Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 2
Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 2

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

Ba a samu nasara ba – Muhammad dandattijo

Muhammad dandattijo Malumfashi: “Ni dai a ganina, yadda al’amura suka kasance a Najeriya, bayan dawowar mulkin dimokradiyya shekaru 14 da suka gabata, babu wata nasara ko ci gaba da aka samu. Mu duba yadda tattalin arzikin kasa ya lalace, cin hanci da rashawa da rud-da-ciki da dukiyar kasa da suka yi yawa. Masu mulki ne kadai ke mallake dukiyar kasa. Ga shi babu ingantacce da wadataccen ruwan sha, babu wutar lantarki. Ga yadda ake tafiyar da mulkin kama-karya, babu zaman lafiya, sai kashe al’umma ake yi babu adadi.
Siyasa dai a Najeriya, idan dai haka take kuma haka za ta ci gaba da tafiya, to zan iya cewa ba ta da wani amfani, domin kuwa babu wani abu da ake samu na ci gaba sai tashin hankali. A Kudancin Najeriya, an mayar da sace mutane da yin garkuwa da su ba a bakin komai ba.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50