Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 3
A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka: Dimokuradiyya gara jiya da yau – Alhaji […]
A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Dimokuradiyya gara jiya da yau – Alhaji Muktari
Alhaji Muktari Ahmad Sheka: “Hakika, cikar mulkin demokradiyya a kasar nan shekara 14 a nawa ra’ayi, gaskiya gara jiya da yau. Idan ka duba yadda aka kassara Arewa wajen kasuwanci da kuma sauran harkoki na rayuwa, ga dokar ta baci. A Arewa yanzu haka idan da za a yi kuri’ar jin ra’ayin jama’a a kasar nan, a tambaye su da mulkin demokradiyya da na soja wanne ya fi? Ina mai tabbatar maka masu ra’ayin mulkin soja ya fi yawa; su ne za su yi rinjaye. Iyakar gaskiyata, ni gara jiya da yau.”