Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 4

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka: Ci baya aka samu a Najeriya – […]

Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 4
Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 4

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

Ci baya aka samu a Najeriya
– Abdulrahman Murtala

Abdulrahman Murtala Bello: “Hakika, shekara 14 da mulkin demokradiyya a Najeriya, ni babu abin da zan ce illa dai Inna lillahi wa inna Ilaihi raji’una. Dalilina na fadin haka kuwa, demokradiyya illar da ta kawo mana ta fi alherin da ta jawo mana, idan muka duba fage daban-daban. Misali, mu dauki rashin tsaro kansa da kuma rashin aikin yi, musammanm atasa da suka gama jami’o’i da manyan kwalejojin ilimi, suke zaune a gidajen iyaye babu aikin yi; duk kuwa da ikirarin guraben samar da aayyukan yi da Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi a kwanan baya. Bugu da kari, kwashe dukiyar talakawa daga baitulmalin gwamnati, babu abin da za mu ce sai ci baya aka samu ba kadan ba.”

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna